Kano Pillars Sun Sayar Da Nzube Sun Sayo Amia Kenneth

227

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayar da dan wasansu na tsakiya wato Nzube inda ya kwashe shekaru biyu a kungiyar.

Mai magana da yawun kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars wato Rilwanu Idris Malikawa garu ne ya bayyana hakan.

Nzu yana daga cikin tawagar ‘yan wasan Kano Pillars dasuka lashe gasar Aiteo ta bana.

Kungiyar ta Kano Pillars ta godewa wannan dan wasa bisa gudun mawar daya baiwa kungiyar kuma sunyimasa fatan alkairi.

Ahannu guda ma kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars ta maye gurbin dan wasan data sayo da Amia Kenneth daga kungiyar kwallon kafa ta Lobi Stars.

Wannan dan wasa da Kano Pillars ta sayo dan wasan tsakiya ne shima.

Malikawa ya bayyana cewar wannan dan wasa ya rattabawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars hannu har tsawon shekaru biyu.

Wannan dan wasa Amia Kenneth ya bayyana cewar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ganshi ne alokacin da ku kungiyarsa take fafata wasan gasar share fage wato pre season da kungiyar Mountain Of Fire na Lagos inda Pillars suka ganshi suka nuna sha’awarsu ta dsukansa.

Wannan dan wasa tsohon dan wasan kungiyar Golden Eaglet ne kuma tuni yabi sahun ‘yan wasan Kano Pillars wajen daukan horo.

Amadadin shugabannin wannan kungiya da masu horas wa da magoya baya sunyimasa barka da zuwa wannan kungiya ta Kano Pillars.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan