Za A Rantsar Da Onoja A Matsayin Sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

141

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayar da sunan Edward Onoja, abokin takararsa a zaɓen gwamna da za a ranar 16 ga Nuwamba a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.

An gano cewa gwamnan ya aika da sunan Mista Onoja zuwa ga Majalisar Dokokin Jihar don tabbatarwa, bayan nan kuma za a rantsar da shi ranar Asabar.

Wannan ci gaba yana zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta tsige Simon Achuba bisa zargin sa da rashin ɗa’a.

Mista Achuba ya fara takun saƙa da Gwamna Bello jim kaɗan bayan an rantsar da shi.

Na hannun damar Gwamna Bello, an ceMista Onoja ya fi kowa faɗa a ji a cikin kwamishinonin gwanan.

Wasu majiyoyi suka ce suna da dangataka tun kafinBello ya zama a 2015.

Ɗan shekara 44, kuma ɗan asalin Emonyoku Ogugu ta ƙaramar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi, Masanin Ilimin Ƙarƙashin Ƙasa ne.

Shi ne babban jami’in bada dabarun cin zaɓe a Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Bello a 2015 kuma shi ne Daraktan Jiha na wata ƙungiyar matasa mai suna Youth Arise Group, ƙungiyar da ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari yaƙin neman zaɓe a 2015.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan