Akwai Yiwuwar ASUU Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

177

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, tana shirin shiga wata sabuwar taƙaddama da gwamnatin Nijeriya bisa abinda ta kira ƙoƙarin ƙaƙaba wa mambobinta Dunƙulallen Tsarin Tattara Bayanai da Biyan Albashin Ma’aikata wato IPPIS.

Shugabannin ASUU sun kira wani taron tattaunawa na gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta ASUU, NEC, inda suka amince cewa ƙungiyar za ta fara sanar da mambobinta don ɗaukar mataki a kan gwamnati.

Tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin cewa duk malamin da ba ya kan tsarin IPPIS ba zai samu albashi ba.

A ranar Lahadi, Shugaban ASUU, Reshen Jami’ar Ibadan, Farfesa Deji Omole, ya ce ASUU ba wai tana yaƙi da adalci ba ne, amma za ta yaƙi duk wani yunƙuri daga gwamnati da ya ci karo da dokokin da ake yin aiki da su da kuma ‘yancin jami’o’i.

Mista Omole ya ce ASUU ta yi tayin taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen tsara taswirar da ta dace don magance matsalolin malaman jami’o’i a tsarin na IPPIS.

Amma Mista Omole ya ce gwamnati tana shirin yin amfani da abinda ya kira Taswirar Tatsar Ma’aikata ta Bankin Duniya.

Ya ce wannan tsari na gwamnati zai bautar da malaman jami’o’i saboda shirin ba shi da tanadin biyan ariyas na ci gaba, alawus na hutun karatu, alawus na aiki da sauransu.

A ta bakinsa, an tsara wannan taswira ce ta gwamnati don a yi fatali da malaman jami’o’i da suka haura shekara 60, wanda ya ce ya saɓa wa sabuwar manufa inda farfesoshi ba za su yi ritaya ba har sai sun kai shekara 70.

Mista Omole ya ga baiken gwamnati bisa zargin ta da shigo da manufofi da suke kawo cikas wajen tafiyar da jami’o’i yadda ya kamata.

“Ƙaƙaba tsarin IPPIS a kan ma’aikatan jami’a saɓa dokar ‘yancin jami’a ne. Saboda haka ya saɓa doka. Yayinda ASUU ba ta yaƙi da adalci a ɓangaren masu tafiyar da jami’a, bai kamata a ƙyale gwamnati ta lalata tsarin jami’o’in gwamnati ba a yaƙi da cin hanci da take cewa tana yi.

“Ya kamata mambobinmu su jajirce su mayar da hankalinsu waje ɗaya a gwagwarmayarmu ta kare jami’o’in gwamnati ta hanyar bijire wa ƙaƙaba tsarin IPPIS a kan malaman jami’o’i”, in ji ƙungiyar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan