Nan Da Makonni Uku Farashin Shinkafa Zai Faɗi Ƙasa Warwas- Manoma

54

Masu siyan shinkafa ka iya samun ragi a farashin na shinkafa zuwa N9000 a buhu mai nauyin 50kg nan da makonni uku masu zuwa saboda manoman shinkafa sun samu amfani mai yawa, a cewar wani rahoton jaridar THE PUNCH.

Manoma da masu casar shinkafa sun ce nan bada daɗewa ba za su cika kasuwanni da shinkafa su kuma rage farashinta sosai biyo bayan samun amfanin gona mai yawa.

Wannan dai yana zuwa ne bayan watanni da aka yi ana fama da tashin farashin shinkafa wanda rufe bakin iyakokin ƙasar nan ya jawo, abinda ya hana shinkafa ‘yar waje shigo wa ta waɗannan iyakoki ta ƙasa.

Tun lokacin da Gwamnatin Tarayya ta rufe kan iyakoki, an samu rahotannin dake cewa wasu mutane sun fara ɓoye shinkafa, suna siya tare da ajiye shinkafa mai ɓuntu da wadda aka casa.

Manoma, waɗanda suka tabbatar da cewa wannan ɗabi’a ce ta jawo tashin farashin shinkafa, sun faɗa wa wakilin THE PUNCH ranar Asabar cewa sun samun amfani mai yawa, kuma wannan zai iya sa a samu gagarumin ragi a farashin shinkafa ‘yar gida nan da makonni uku.

A wata tattaunawa da ya yi da THE PUNCH ranar Asabar a Abuja, Shugaban Ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Ƙasa, RIFAN, Aminu Goronyo ya ce: “Mun samu amfanin gona da ba mu taɓa samu ba. Ba mu taɓa samun amfanin gonar da muka samu ba wannan shekarar”.

Ya kuma ce binciken da RIFAN ta yi ya gano cewa wasu mutane suna shirye-shiryen sa shinkafa ta yi ƙaranci a dukkan faɗin ƙasar nan don biyan buƙatun kansu.

Mista Goronyo ya ce koda yake dai akwai ƙarancin shinkafa a wasu ‘yan wurare da wasu suka haifar da gangan, abinda ya jawo ƙarin farashi, hakan ba zai ɗauki lokaci mai tsawo ba.

“Akwai maƙiyan ƙasar nan waɗanda ke siya da ajiye wannan shinkafa kawai don suna so su haifar da ƙarancin shinkafa na ba gaira ba dalili. Amma bari in faɗa maka, amfaninu yana zuwa nan da mako biyu zuwa mako uku masu zuwa, kuma samfarerar da za ta zo kamfanonin casar shinkafa, masu casar shinkafar da muke da su ba za ma su iya cashe ta ba”, in ji Mista Goronyo.

“Duk irin ƙoƙarin ɓoye ko haifar da ƙarancin shinkafa na ba gaira ba dalili kamar yadda aka gani a wasu wurare, waɗannan mutane za su sha kunya”, ya ƙara da haka.

Ya ci gaba da cewa: “Waɗannan mutane ba za su iya siye samfarerar da za ta zo kamfanonin casar shinkafa ba, kuma muna da abinda ya wuce buƙatun ‘yan Najeriya”.

Bincike ya nuna cewa farashin shinkafa ‘yar gida a Abuja ya tashi daga N14000 da ake siyar da ita watanni biyu baya zuwa N16,500 da N19000, ya danganta da kasuwa.

A farkon wannan wata, THE PUNCH ta kawo rahoton cewa a manyan kasuwanni a Legas, farashin wasu kayayyakin abinci da suka haɗa da shinkafa ya ƙaru da kaso 42 cikin ɗari zuwa kaso 100 cikin ɗari daga Agusta lokacin da aka rufe boda zuwa makon ƙarshe na Satumba.

Rahoton ya ce a kasuwannin Ille Epo, Daleko, Mile 12, Isheri da Ogba, dukkaninsu a Legas, buhun shinkafa ‘yar waje mai nauyin 50kg da ake siyarwa tsakanin N13000 da N14000 a da, ya tashi zuwa N24000 da N30000, yayinda buhun shinkafa ‘yar gida mai nauyin 50kg ya tashi daga N14000 zuwa N18000.

Amma Mista Goronyo ya ce mambobin RIFAN sun yanke shawarar daina siyar wa ɗaiɗaikun mutane samfarera idan ba masu casar shinkafa ba ne, yana mai nanata cewa su ne suka haifar da rashin farashin.

Ya ce: “Mun lura da cewa da akwai mutane da suke shiga kasuwa don siyan samfarera waɗanda ba masu casar shinkafa ba ne. Ba mu san daga ina suka zo ba. Maƙiya wannan ƙasa ne saboda suna so sa Najeriya a wani hali inda za mu haifar da ƙarancin shinkafa na ba gaira ba dalili.

“A yanzu muna ɗaukar matakai don shawo kan wannan matsala. Ba wani mai siyan samfarera da zai zo wajen manoma kai tsaye ya siya har sai ya ba mu shaida. Za a samu mai shiga tsakani wanda zai tantance mai siyan don ya sani shi mai casar shinkafa ne ko kuma a’a. To, wannan shi ne abinda muke ƙoƙarin yi yanzu”.

Lokacin da aka tambaye shi ya faɗi farashin da za a iya siyar da shinkafar ‘yar gida a makonni masu zuwa, Mista Goronyo ya ce burin manoma da masu casar shinkafa shi ne su rage farashin buhu mai nauyin 50kg zuwa N9000.

“Alƙawarin da muka yi shi ne ‘yan Najeriya za su ci gaba da siyan shinkafa a farashi mai rahusa kuma za ta samu. Kuma kamar yadda na faɗa maka, har yanzu muna siyar da buhu ɗaya na samfarera a N7,500, masu casa kuma suna siyarwa a N14000”, in ji shi.

Shugaban na RIFAN ya ƙara da cewa: “Ba na tunanin farashin zai tashi, abinda ma muke fata shi ne farashin zai ci gaba da yin ƙasa, kuma ba shakka zai sakko. Wasu daga cikin masu casar da muke da su suna siyarwa a N12000, kuma muna fatan ‘yan Najeriya za su siyi buhun shinkafa mai nauyin 50kg da aka casa tsakanin N9000 zuwa N10000”.

Mista Goronyo ya ce dillalai a hada-hadar shinkafa sun yi wani taron ganawa da Babban Bankin Najeriya, CBN, a kwanan nan, inda suka cimma matsaya a kan wasu manyan batutuwa.

“An yi mitin kimanin makonni biyu da suka gabata da ya haɗa da manoma, masu casar shinkafa da CBN inda aka aminci cewa ba za a samu ƙari a farashi ba”, in ji shi.

Haka kuma, Ƙungiyar Masu Casar Shinkafa ta Ƙasa, RIMAN, ta tabbatar da wannan mitin, ta kuma bayyana cewa Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi kira ga dillalai da kada su tashi farashi sakamakon rufe bakin iyakokin ƙasa.

Mista Emefiele ya faɗa wa dillalan shinkafar cewa an rufe bakin iyakokin ƙasar nan ne don a bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya, a kuma tabbatar da cewa ƙasar nan tana iya ciyar da kanta a hada-hadar shinkafa.

Waɗanda suka halarci mitin ɗin sun tattauna kan yadda za a inganta samar da shinkafa a kuma hana ɓoye ta da ƙara farashi, kamar yadda wani daftarin abubuwan da aka cimma a taron ganawar, wanda RIMAN ta ba wakilin THE PUNCH ya nuna.

Shugaban RIMAN, Peter Dama, ya ce masu casar shinkafa suna goyon bayan rufe bakin iyakokin Najeriya, ya kuma yi kira ga gwamnati da kada ta saurari masu matsin lamba da suke so a janye wannan manufa.

Ya kuma nuna ƙyama game da ɗabi’un da suka haifar da samun tashin farashi, sannan ya nemi a tallafa wa mambobin RIMAN da kuɗi don su ƙarfafa kansu, su kuma faɗaɗa harkokinsu na casar shinkafa don ƙara bunƙasa noman shinkafa.

Shugaban na RIMAN ya ce abubuwan da aka cimma a taron ganawar za su taimaka wajen ƙarin farashi na ba gaira ba dalili, kamar yadda ya ce farashin shinkafar ‘yar waje kaɗai ya ƙaru.

Mista Goronyo ya ce: “Mun yi taron tattaunawar ne a makon da ya wuce da masu casar shinkafa da masu siyarwa a dukkan faɗin ƙasar nan kuma sun fahimtar da mu cewa farashi daga ɓangarensu har yanzu yana nan yadda yake.

“Ko kwabo ɗaya ba mu ƙara ba a farashin casasshiyar shinkafarmu. Haka kuma, su (masu casar shinkafa) ba su ƙara farashin casasshiyar shinkafar da ko kwabo ɗaya ba. Farashin shinkafa ‘yar waje kaɗai za ka ce ya tashi. Amma kada shinkafa ‘yar waje ta ruɗi ‘yan Najeriya wadda ba ta kai daɗin tamu ba idan aka kwatanta”, in ji shi.

Lokacin da aka faɗa masa cewa ana siyar da shinkafa ‘yar gida tsakanin N16,500 da N19000 ya dogara da kasuwa, maimakon farashin N14000 watanni biyu da suka gabata, sai Shugaban RIFAN ya ce manoma ba su canza farashinsu ba.

“Har yanzu N14000 ce, saboda kamar yadda na ce, mun yi taron ganawa da Babban Bankin Najeriya makon da ya gabata. Farashin da manomanmu ke siyarwa har yanzu shi ne N7,500 buhu mai nauyin 75kg, wanda idan aka yi masa casa, zai ba ka 50kg na shinkafa. Har yanzu farashin shinkafa yana nan tsakanin N13,500 da N14000 daga masu casar shinkafarmu”, a cewar sa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan