Adam Zango Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗalibai 101, Ya Biya Musu Naira Miliyan N46

50

Adam A. Zango, shahararren jarumin fina-finan Hausar nan, ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai 101, inda za su yi karatu a Professor Ango Abdullahi International School, Zaria.

Shugaban Kamfanin Shirya Fina-Finai na Prince Zango Production, Nigeria Limited, Mista Zango ya biya zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan N46.75 a matsayin kuɗin karatun shekara uku.

Mista Zango ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Ina jin abu ne mafi kyau samun damar taimaka wa da tallafa wa wasu waɗanda ba su da dama. Taimakon mutane musamman yara yana cika zuciyata, kuma wani abu ne da nake jin daɗin yi. Wace irin gudummawa ka ke bayarwa, ko kuma wani irin tasiri ka ke yi a rayuwar wasu? A kullum mukan yi iya yin mu don cimma abubuwa manya. Daga yanzu, ni da ‘yan tawagata, ba za mu ci gaba da ɓoye kyawawan ayyukanmu ba, za mu yi aiki don inganta rayuwar mata da marasa galihu, manya da iyalai a dukkan faɗin Najeriya”.

Shugaban Makarantar, Malam Hamza Jibril ya tabbatar da wannan ci gaba.

“Gaskiya ne Adam Zango ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai 101 a makarantarmu. Mafi yawan ɗaliban marayu ne da marasa galihu”, in ji shi.

A kwanan nan ne Mista Zango ya sanar da ficewarsa daga Kannywood.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan