Yadda Aka Samu Gawar Sojan Najeriya A Ƙarƙashin Gada A Abuja

237

An samu gawar VL Henry, wani jami’in Rundunar Sojin Najeriya a ƙarƙashin wata gada a Abuja.

An samu gawar sabon sojan mai muƙamin laftanar na biyu a Gadar Mabushi da misalin ƙarfe 8:40 na safiyar Talata, a cewar majiyar sojoji.

Wani shaidar gani da ido ya ce an samu gawar sojan ne tare da katin shaidar aikin soja da raunuka da dama a kansa.

Har yanzu masu magana da yawun Rundunar Soji da ta ‘Yan ba su ce komai ba game da al’amarin, amma wasu jami’ai da suka yi magana kuma suka roƙi a sakaye sunayensu saboda ba a ba su izinin magana da kafafen watsa labarai ba sun ce ana ganin mutuwar sojan ka iya zama kashe kai wata ƙila saboda rashin jituwa da ya faru tsakanin jami’in da wasu mutane da ba a sani ba ko kuma hari daga mahara cikin dare.

Mutuwar Mista Henry ta zo ne ‘yan kwanaki kaɗan bayan ya kammala wani kwas na yaƙin ƙasa a Kalabar ranar 18 ga Oktoba.

Ya yi aiki a Nigerian Army Division 3 Provost Group a Jos.

Tuni an binne gawarsa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, Gwagwalada, a cewar majiyoyi.

Ba a sani ba dai ko an kammala bayar da sanarwar magajinsa, kamar yadda dokar aikin soja ta tanada.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan