Koda yake kafin kafuwar Majalisar Ɗinkin Duniya akwai wasu ƙungiyoyi da aka kafa domin haɗin kai da cigaban ƙasashen duniya, irin su ƙungiyar ma’aikatan sadarwa ta ƙasa da ƙasa a 1865 da kuma ƙungiyar ma’aikatan gidajen wasiƙu a 1874. Waɗanda daga bisani suka rikiɗe zuwa hukumomin Majalisar ta Ɗinkin Duniya bayan da aka kafa ta.
Taron farko da aka gudanar a ƙarƙashin lemar Majalisar Ɗinkin Duniya shi ne wanda aka gudanar a birnin Hague. Wannan taro dai shi ne ya kai ga kafa kotun duniya dake birnin na Hague a ƙasar Holland a 1902.
A shekarar 1945 ne ƙasashen duniya 50 suka gudanar da taro a Jihar San Francisco ta Amurka domin ƙaddamar da dokoki ko jadawalin aiyukan Majalisar Ɗinkin Duniya. Manyan ƙasashen duniya da suka rattaba hannu a wannan yarjejeniyar dai sun haɗa da Amurka da China da Tarayyar Rasha da Birtaniya da kuma Faransa , waɗannan ƙasashen ne kuma daga bisani suka zama wakilai na dindindin na masu ƙarfin faɗa aji.
A ranar 24 ga watan Oktoban 1945 ne dai waɗannan ƙasashe suka rattaba hannu a daftarin ƙarshe da ya kafa Majalisar ta Ɗinkin Duniya, abinda ma yasa a duk ranar 24 ga watan na oktoba Majalisar ke bikin zagayowar ranar da aka kafa ta.
Kuma a bana Majalisar ta cika shekaru 74 da kafuwa. Kuma tun bayan kafuwar ta tayi shugabanni da dama kuma na baya bayan nan sune Butrus Butrus Ghali daga Masar da Kofi Annan na Ghana da kuma Ban Ki-Moon daga ƙasar Koriya ta Kudu, sai Antonio Gutteres daga ƙasar Portugal