Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta shiriya tsaf don gurfanar da Abdulrashid Maina, tsohon Shugaban Kwamitin Ko-ta-kwana na ‘Yan Fansho, PRTT a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Jami’an EFCC sun isa kotun da Mista Maina da ɗansa da ya nemi arcewa, Faisal da misalin ƙarfe 8:52 na safiyar Juma’ar nan.
Ana zargin sa da hannu a badaƙalar kuɗin ‘yan fansho da suka kai zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 100.
Tun a farkon wannan mako, wata Babbar Kotu ta bada umarnin ƙwace wasu kadarori 23 da su ke mallakinsa.
Turawa Abokai