Ƴan Najeriya Na Kusa Da Samun Tabbatacciyar Wutar Lantarki – Buhari

254

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa al’ummar ƙasar nan tabbacin samun wutar lantarki mai ɗorewa kuma cikin sauki nan ba da daɗewa ba. Shugaban ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar kawo sauyi a ma’aikatar wutar lantarki.


Shugaban dai yana wannan jawabin ne a daidai lokacin da tallafin kuɗin lantarki a zamanin mulkin gwamnatinsa ya doshi sama da naira triliyan ɗaya, a cikin shekaru biyar.


“muna shirin sauya yadda ake tafiyar da ma’aikatar wutar lantarki. A watan Agusta na wannan shekarar, mun ƙaddamar da shirikan wutar lantarki domin zamanantar da ƙasar nan a tsarin rukuni kashi uku: farawa daga gigawats 5 zuwagigawats 7, sai kuma gigawats 11 a cikin shekarar 2023, sannan daga karshe a samar da goma 25” in ji shugaba Buhari.


A ƙarshe shugaba Buhari ya ce jagoranci nagari da bunƙasar tattalin arziki ba za su tabbata ba, ba tare da zaman lafiya mai ɗorawa ba da ingataccen tsaro da kuma aminci a kasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan