Hukumar Hisbah A Jihar Kano Ta Kame Karuwai Guda 70 A Bichi

545

Jami’an rundunar hisbah a jihar Kano sun kai sumame kasuwar Badume da ke yankin ƙaramar hukumar Bichi in da ake hada hadar kasuwancin tumatur, a gefe guda kuma Mata masu zaman kan su suka kafa Shaguna domin sheƙe ayarsu.

A lokacin gudanar da wannan sumame dai rundunar ta samu nasarar kame mata masu zaman kansu har guda 70, yayin da aka kame maza suma guda 23 in da suka zama jimla 93.

Bayan kamun da aka yi musu rundunar ta gano cewa mutum 24 ne kawai ƴan asalin jihar Kano, yayin da sauran guda 69 din sun zo ne daga wasu jihohi daban daban, sai kuma mutum 4 da aka gano cewa ƴan asalin jamhuriyar Nijar ne.

A yanzu haka dai ana ci gaba da yi musu gwaji domin tantance lafiyarsu a babban ofishin hukumar hisbah da ke Sharaɗa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan