Ƴan Bindiga Sun Harbe Limamin Masallacin Juma’a A Taraba – JIBWIS

179

Wasu yan bindiga dadi da muke kyautata zato masu Garkuwa da mutanene, ko kuwa barayin hanya ne Sun harbe Malam Gambo mutum daya, akan hanyar GONARSA dake tsakanin hanyar iware zuwa jalingo.

Malam Gambo mutumin kirki ne wanda Rayuwarsa kashi 90% na Rayiwanshi Akan neman ilimine dakuma Karantarwa.

Malam yana daya daga cikin manyan daliban Dr Ibrahim Jalo jalingo kuma Abokin Da’awan sa.

Malam bashida yawan magana saboda kiyaye Harshe sai Akan abinda yazama dole.

Sannan Malam shi ne limamin masallacin Juma’a na Anguwan Kasa, Baiwuce Wata dayaba Aka sauya mai masalaci zuwa masallacin Juma’a na techno bat jalingo.

Da safiyar yau litinin 29/02/1441# 28/10/2019 in Allahu za’ayi zana’izar malam à babban masallacin Juma’a na bin fodio, inda Dr Ibrahim Jalo ke limanci, Da Misalin karfe 9:30 zuwa 10:00am.

JIBWIS JALINGO.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan