Home / Gwamnati / Buhari Zai Wuce Landan Daga Saudiyya

Buhari Zai Wuce Landan Daga Saudiyya

Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai wuce Landan, UK bayan ziyarar aiki da zai kai Riyad, babban birnin Saudiyya.

A ranar Litinin ne Shugaba Buhari zai bar Abuja don halartar Taron Tattalin Arziƙi na Future Investment Initiative, FII a Riyad.

A gefen taron, Shugaba Buhari zai tattauna da Mai Alfarma, Sarki Salman bin Abdul’aziz na Saudiyya da Mai Alfarma, Sarki Abdullah II na Jodan.

“A ranar Laraba, 30 ga Oktoba, 2019, Shugaban Ƙasa zai halarci Babban Taro mai taken “Mene Ne Abu Na Gaba Ga Nahiyar Afirka: Ta Yaya Zuba Jari Da Kasuwanci Za Su Canza Nahiyar Zuwa Babbar Nahiya Mai LabarinTattalin Arziƙi Mai Nassara Ta Gaba?” da Shugabannin Ƙasashen Kenya, Congo-Brazzaville da Burkina Faso.

“A ƙarshen Taron Ƙolin, Shugaba Buhari zai wuce Ingila ranar Asabar, 2 ga Nuwamba, 2019 bisa ziyarar ƙashin kai. Ana sa ran zai dawo Najeriya ranar 17 ga Nuwamba, 2019”, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Femi Adesina ya sanya wa hannu.

About Hassan Hamza

Check Also

Ya Kamata CBN Ya Biya Kuɗi A Ceto Ɗaliban Jami’ar Greenfield Ta Kaduna— Sheikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan, Sheik Ahmad Gumi, ya yi kira ga gwamnati da kada …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *