Ruwan Sama Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 7 A Saudiyya

167

A ƙalla mutum bakwai ne su ka rasa rayukansu, wasu 11 kuma su ka jikkata sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ambaliyar ruwa da aka samu a Yankin Gabas na Saudiyya, Ma’aikatar Kare Farar Hula ta Saudiyya ta bayyana haka ranar Litinin.

An samu waɗannan mace-mace da jikkata ne a lardin Hafar al-Batin sakamakon fara ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi tun ranar Juma’a har zuwa Lahadi da daddare, Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya, SPA, ya jiyo wani mai magana da yawun Ma’aikatar Kare Farar Hula ta Saudiyya yana faɗar haka.

Mai magana da yawun ma’aikatar ya ƙara da cewa an kwashe mutane 16, an ba bakwai matsuguni, sannan ababen hawa 40 da gidaje uku sun lalace.

Ruwan ya tsare mutane da dama da wani abin hawa guda, a cewar rahotonni da Ma’aikatar Kare Farar Hular ta samu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan