Anyi Ruwan Kwallaye Afilin Anfield Agasar Carabao

148

Anyi ruwan kwallaye afilin wasa na Anfield tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Arsenal.

Domin kuwa kafin ayi bugun daga kai sai mai tsaron gida antashi wasa kowacce kungiya nada ci 5.

Kwallayen dai andinga yin jefa min na jefamaka inda tun ana 5 da 4 gaf da za a tashi awasa Liverpool suka rama kwallonsu ta 5.

Daga bisani ne dai kungiyoyin kwallon kafan guda biyu sukayi bugun daga kai sai mai tsaron gida a tsakaninsu inda kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe Arsenal daci 5 da 4.

Ayanzu dai ta tabbata cewar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tasami tikitin buga wasan gaba inda kuma Arsenal saidai su tara awata shekarar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan