Kamfanin MTN ya ce ya toshe layuka 600,000 bisa bin umarnin Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Ƙasa, NCC, na rufe layuka marasa cikakkiyar rijista.
Kamfanin ya samu masu amfani da layuka miliyan 61.6 a daga watan Yuli zuwa Satumba, inda ya samu ƙarin mutane 100,000 a duk bayan wata uku, rahoton watanni uku na kusa da watanni ukun ƙarshen shekara da ba a tantance ba ya bayyana haka ranar 30 ga Satumba, 2019.
A rahoton da aka wallafa ranar Laraba, MTN ya ce kuɗin shigarsa ya ƙarun da kaso 12.1 cikin ɗari zuwa N854bn, wanda ƙarin kaso 10.1 da kaso 34.9 cikin ɗari daban-daban suka haifar.
Rahotan hada-hadar kuɗin ya bayyana cewa ribar kowane hannun jari ta ƙaru da kaso 29 cikin ɗari zuwa N7.29 yayinda kuɗaɗen manyan ayyuka, ‘capex’, suka ƙaru da kaso 39.5 cikin ɗari zuwa N154.1 bn.
MTN ya ce kasuwancinsa na fasahar hada-hadar kuɗi, wato ‘fintech business’, ya samu karɓuwa a wajen abokan ciniki da kaso 21.7 cikin ɗari shekara bayan shekara ƙarin kuɗin shiga, wanda tsarin Xtratime ya haifar, tsarin dake ba masu amfani da layuka su ci bashin kuɗin kira.
Kamfanin ya ce ya ƙaddamar da tsarin Super Agent Services a Agusta, 2019, ya kuma samu wakilai masu rijista 66,000.
Da yake jawabi game da hazaƙar kamfanin, Shugaban Kamfanin na Najeriya, Ferdi Moolman ya ce MTN ya samu riba ta lamba biyu-biyu duk da ƙalubalen kasuwanci.
[…] Muƙalar Da Ta GabataMTN Ya Toshe Layuka 600,000 […]