Allah cikin hikimarsa a duk sanda zai turawa wata al’umma manzo, ya kan tura wanda zai wahala a yi saurin yarda da shi. Idan mu ka dauki kakanmu annabi Ibrahim an tura shi ya kira mutanensa da su ke kan bautar gumaka kuma shi ya kasance daga cikin gidan shugaban wannan bauta. Haka shi kuma annabi Musa, sai aka tura shi wajen fir’auna wanda ya dauke shi a matsayin dansa na cikinsa ya rene shi a matsayin dan sarki.
Annabi Isa kuwa sai ya fito daga gidan shehunnai na Imrana, amma ya kasance al’ummarsa na daukarsa a matsayin shege domin bashi da uba. Annabi Muhammadu kuwa ya kasance maraya, talaka duk da cewa ya fito daga babban gida na Abdulmutallib.
Dalilin da Allah ke tura mutane wadanda da wahala al’ummarsu su yarda da su kai tsaye, shine saboda ya na son mutane su yi imani bisa doron hujja da yakini ba don wata alaka ba. Duk wanda ke son gaskiya kadai ke iya amincewa da da’awar manzanni. A yau da ace Allah zai turowa Hausawa manzo, ina tsammanin da sai mu ga wani Inyamuri kawai ya zo da da’awar cewa shi manzo ne, ka ga kuwa idan ba mai son gaskiya ba da wahala wani bahaushe ya bar addininsa ya bi na Inyamuri. To amma kasancewar an rufe kofar sabon sako daga ubangiji wajibinmu ne mu koma kan wanda ya ke hannunmu mu yi aiki da shi.
Ba na mantawa a lokacin da ina dan karamin yaro muna karanta littafin Arba’una Hadith, akwai wani hadisi wanda Manzon Allah ke wa wani yaro nasiha, wannan yaron shine Ibn Abbas inda ya ke ce masa “Ya kai yaro! Idan za ka so mutum ka so shi domin Allah haka nan idan za ka ki shi ka ki shi domin Allah” Hakika wannan nasiha ta annabi na dada jaddada umarnin Allah a cikin Qur’ani inda ya ke cewa Q4:135 “Ya ku wadanda kuka yi imani! Ku tsayu da shaida domin Allah ko da a kan ku ne ko a kan mahaifanku ko makusanta, ko kuma mawadata ko mataulata” wannan aya ita ce kololuwar adalci, abinda ya sa har wadanda ba musulmi ke tunkaho da ita domin Jami’ar Harvard da ke Amurka ta kafe wannan ayar a kofar shiga sashen nazarin shari’a na wannan jami’a. (Shin zamu iya kafe ayar Bible a jami’ar Ummul Qura da ke garin Makka?). Cikar adalci shine a lokacin da ka tsaida shi a karan kanka, ko a kan mafi kusanci da kai, kuma da ace Hausawa sun rungumi koyi da wannan aya da hakika ba mu shiga cikin tsaka mai wuya da mu ke fuskanta a yanzu ba.
Gazawarmu wajen yin aiki da wannan koyarwa ya haifar mana da halaye guda biyu wadanda su ka zamar mana dabaibayi da ya hana mu motsawa ko nan da can. Da farko mun gadar wa kanmu kare shugabanni a doron kabilanci, duk kuwa irin iliminmu da wayeyarmu, bama gaza yin farat wajen kare manyanmu a doron kabilanci ba a doron adalci ba. Abu na biyu kuma shine duk wani abu da ya shafi addini sai mu yi ca a kai ba tare da la’akarin adalci ko rashin adalci ba. Sakamakon haka sai shugabanninmu su ka sami damar yin sharafinsu saboda masaniyar komai za su yi akwai wadanda za su fito su goya musu baya. Sannan a duk sanda su ke son cimma wani muradi nasu sai su cuso banbancin addini, sanin cewa zamu tada jijiyoyin wuya ba tare da duba kowacce irin mahanga ta adalci ba.
Kakanninmu sun bar mana al’umma wadda su ka tsara kuma su ka rayu cikinta a doron adalci, abinda ya baiwa Hausawa a baya damar yin fice a harkokin kasuwanci yadda su ka zama kashin bayan cinikayyar fatake da ke ratsa hamada (Trans-Sahara) abinda ya nunawa turawa irin tarin arzikin da ke kasashen Afirka wanda ya sa su ka shiryo su ka zo su ka yi mana mulkin mallaka.
Dan Fodio, wanda ya kasance almajiri, ya daga tutar yaki da zalunci inda ya sami goyon bayan talakawa su ka hambare azzaluman sarakunan habe, sannan su ka kafa daular musulunci cikin adalci. Bayan sama da shekaru dari da kafa wannan daula sai jikan Dan Fodio, wato Ahmadu Bello Sardauna shi kuma ya jagoranci yakin neman yancin daga hannun turawa, abinda ya haifar da samuwar sabbin shugabannin al’umma a matsayin Yan Boko. Amma abin takaici shine duk da cewa Sardauna ya kafa harsashin samun ci gaban arewacin Nijeriya ta hanyar ilimin zamani, sai kuma ya barwa magadansa wasu munanan halaye guda biyu wadanda su ne ummul-aba’isin mummunan halin da mu ke ciki a yanzu. Wadanan halaye, wato amfani da kudaden jama’a don biyan bukatar kai ko don siyasa da kuma nuna son kai wajen bada dama ga yan kasa, magadan Sardauna sun dauke su halaye na halal abinda ya jawo tabarbarewar harkokin mulki a arewa. Yan boko, farar hula da sojoji, wadanda su ka dafe madafan iko a kasar tun bayan Sardauna sun riki wadannan halaye a cikin mu’amalar gudanar da ayyukan da aka ba su amana. Don haka magadan Sardauna ne su ka kafa harsashin tabarbarewar komai a kasar nan.
A fahimata ta, babu wata al’umma a Najeriya, ko ince ma a duniya, wadda a cikin shekaru kasa da hamsin su ka lalace irin mu. A baya mun kasance mutane masu darajta ilimi fiye da komai yadda duk da karfin ikon da sarakuna ked a shi, su kan girmama masu ilimi fiye da kowa. Sannan yadda manyan garuruwan mu ke cike da kabilu daban daban babbar shaida ce ta irin yadda muka fi kowa karbar baki. Idan bako ya shigo cikinmu ana hada shi da wanda zai koya masa sana’a kuma cikin dan lokaci kankane ana iya bashi aure yadda zai zama dan kasa. Saboda riko ga sana’o’i da kasuwanci, kowanne gida akwai irin sana’ar da ya ke yi, abinda ya sa a baya mun fi kowa karancin marasa aikin yi. Yara da zarar sun fara iya tafiya ake fara koya musu sana’ar gidansu yadda sana’o’in mu suka yi shura tsawon daruruwan shekaru. Tsarin zamantekawarmu na sarakuna, hakimai, dagatai da masu unguwannin ya bamu cikakken tsaro yadda ba wani bako da zai shigo kasa ba’a san daga ina ya ke ba, kuma me ya zo yi. A da idan mutum ya yi abin kunya da kansa ya ke guduwa ya bar gari, sannan al’umma na hade kai su kyamaci duk wani mai mummunan hali, abinda ke kowaya matasa su kyamaci munanan halaye. Duk al’adu da halayenmu masu kyau mun yi watsi da su saboda son duniya da son kai. Idan kuma akwai wani abu da ya gama rusa wannan al’umma ta mu shine hassada. Hassada ta zama ruwan shan mu da kuma iskar shakar mu, domin mun daina ganinta a matsayin uwar duk wani sharri da zunubi, mun rungume ta yadda kowannenmu ke yin ta ba tare da sanin ma ya na yin ta ba. Hassada ita ta haifi duk wani sabo, saboda mun ga yadda ta tunzura shaidan ya gagara rusuna wa Adam abinda ya jawo koro mu doron duniya. Hassada ta shallake mazaunin da aka san ta, wato tsakanin abokai da yan uwa ta haura zuwa ga tsakanin Uba da da, Uwa da ya, tsakanin mata da miji kai har ma tsakanin mutanen da su ka hadu na wani gajeren lokaci, misali a kan hanya ko a layin Banki. Ina kyautata zaton da mutum zai iya samun jerin al’ummomi da shedan ya saka a gaba wajen ya cimma musu, ban tsammanin za’a ga hausawa a sahun farko sai dai a kurar baya domin shedan ya san cewa ya siyar mana da hassada mun biya har da la’ada, don haka ba ya bukatar mai da hankali kan mu, domin ya san cewa hassada za ta yi masa aikinsa.
Yan Boko da manya a al’ummarmu sun fi kowa iya bayanin yadda al’amura su ka lalace sannan idan su na zayyana maka yadda za’a bi a gyara sai ka rantse kamar ma an gyara. Amma a inda gizon ke saka shine idan aka tattaro su domin su hadu su yi aikin wajen aiwatarwa, a nan za ka ga hassada, kyashi da bani-na-iya. Abinda ke hana mu yin komai domin maganin matsalolin mu.
Addini, maimakon ya zama mai cetar mu ya gyara mana halayya sai ya zama jagoran koma bayan mu saboda mun yi watsi da mahimman darussan da ya ke koya mana, sai dai amfani da shi wajen nuna banabnacin da ke tsakaninmu. Ginshikin zaman lafiya a kowacce al’umma bai wuce yin adalci a tsakanin mutane ba, tare da rarraba arzikin al’umma, kamar yadda Zakka ta koya mana. Amma a yau sadaka ta fi zakka kima a cikinmu, wannan ginshiki na imani ya zama koma baya yadda ba wanda ya damu da assasa zakka. Rashin raba zakka da rashin saka kudade cikin ayyuka da za su kawo aikin yi da habaka tattalin arziki shine ginshikin talaucin mu a yanzu. Za ka ga bankunanmu sun dankare kudade a asusun su ba tare da fitar da kudaden wajen habaka tattalin arzikin kasa ba, ta hanyar tallafawa kananan sana’o’i. Duk da cewa a kullum arzikin kasa na habaka, amma sai ga shi yawanci yan kasa na komawa cikin talauci, yadda ake mana lakabi da matattarar talauci a duniya.
Alkalumma suna nuna cewa akwai kimanin kashi 40% zuwa kasha 60% na matasan mu da basa aikin komai, sannan mu ne mu ka fi kowa a duniya yawan haihuwa da kuma cirar tutar mun fi kowa yawan yara da ke bara ko rashin zuwa makaranta. Kididdiga a kan harkar ilimi kuwa, na nuna mun fi kowa yawan masu jahilci. A baya bayan nan mun ga dai yadda Boko Haram ta tasar ma tarwatsa mu, to wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta da abinda zai zo nan gaba matukar muka ci gaba da surutu kawai ba tare da fara neman hanyar magance matsalolinmu na gajere da dogon zango ba.
Ya ku Hausawa, wajibi mu tashi tsaye mu daina zance mu dukufa wajen nemo mafita ga wannan al’umma kuma domin mu gujewa tsinuwar yayan mu da za su zo nan gaba. Matsalolin mu biyu ne, jahilci da talauci kuma hanyoyin magancesu shine samar da ilimi ingantacce da aikin yi ga matasan mu, ko dai mu gaggauta yin haka ko kuma mu kasance cikin bala’in da zai biyo baya. Wajibi mu tashi tsaye don wannan aiki tun kafin lokaci ya kure mana.

Ali Abubakar Sadiq, Dan Jarida Ne Mai Kuma Yin Sharhi Akan Al’amuan Yau Da Kullum. Ya Rubuto Daga Birnin Kano.
Aleesadeeq1@yahoo.com
08039702951
[…] Muƙalar Da Ta GabataHalaye Biyu Da Su Ka Yiwa Hausawa Tarnaki – Ali Abubakar Sadiq […]