Duk Inda Ɓarayin Gwamnati Suka Gudu Sai Mun Kamo Su- Magu

233

Shugaban Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’anati, EFCC, Ibrahim Magu, ya aika da saƙo ga jami’an gwamnatin Najeriya waɗanda suka yi sata daga lalitar gwamnatin ƙasar nan cewa duk inda suke a duniya, doka za ta same su.

Ya aika da saƙon ne a Taron Ƙolin Zuba Jari na ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje na 2019 mai taken: Alkinta Duniyoyin ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje Don Haɓaka Tattalin Arziƙi” ranar Laraba a Abuja.

“Abin fa ba zai zama kamar yadda aka saba da ba; idan ka saci kuɗi a nan ka tafi ka ɓoye a can, za mu bi ka ba tare da wasu tsauraran dokoki ba, mu dawo da kai”, in ji shi.

Ya ce hukumar za ta kare zuba jarin da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje suka yi a ƙasar nan.

Mista Magu ya ce an tsara hurumin EFCC don ƙarfafa gwiwar masu zuba jari, musamman ‘yan ƙasashen waje don su samu Najeriya wani wajen zuba jari mai ɗaukar hankali.

“Ina son in tabbatar wa dukkan ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje cewa za mu yi dukkan mai yiwuwa don kare zuba jarinku.

“Akwai ‘yan Najeriya ƙwararru da yawa a ƙasashen ƙetare waɗanda sun yi abubuwa masu kyau da yawa kuma sun samu dukiya ta halal, waɗanda ke son zuwa nan su zuba jari, kuma mun mayar da hakan wani batu na musamman.

“A halin yanzu, muna aiki a matakin ECOWAS kan yadda za mu iya haɗa kai da dukkan hukumomin kiyaye doka a ƙasashen ECOWAS.

“Za mu gabatar da wata yarjejeniya, za a gabatar da yarjejeniyar ɗin a gaban Shugabannin Ƙasashen Afirka wata ƙila wajen Fabrairu, 2020 za a a gabatar da ita”, a kalamansa.

Mista Magu ya yi jawabi game da tura kuɗi ƙasashen waje a ciki da wajen ƙasar nan.

“Kamar wannan Western Money Union Transfer ya zama matsala saboda idan suka tura wa ‘yan uwansu kuɗaɗe, yadda za su samu kuɗin ya kan zama wahala.

“Bankin zai ce ma ka zo yau, ka zo gobe, a ƙarshe dai, idan ka tura dala dubu biyu da ɗari biyar, daga ƙarshe dala dubu ɗaya za su samu.

“Amma muna aiki tuƙuru ba dare ba rana don kawo tsafta a wannan Western Money Transfer ɗin da sauran tura kuɗaɗe da wasu ma’aikatan bankuna ke amfani da su don damfarar waɗanda ake tura wa kuɗaɗen.

“Za mu share hanya don ya zama abu mai sauƙi a gare ku ku tura kuɗinku ga ‘yan uwanku, kuma su samu”, in ji Mista Magu.

Mista Magu ya yi kira ga dukkan al’umma da su shiga yaƙin da ake yi da cin hanci ko suna ‘yan Najeriya a gida ko suna waje saboda cin hanci yana shafar kowa kai tsaye ko ba kai tsaye ba.

“Wannan ne lokacin da ya kamata ku bayar da gudunmawarku saboda ba za mu iya mu kaɗai ba.

“Don Allah ku taimaka mana da bayani masu amfani, idan akwai wani abu da ba za ku iya yi ba, muna da ikon yin sa ko a wajen ƙasar nan ne, akwai hanyar da za mu iya samun mutum.

“Kuma muna da Ofisoshin EFCC kusan a dukkan ofisoshin jakadancin ƙasashen waje a ƙasar nan, kuma akwai lambobin waya.

“A Intanet, muna aiki kusan da dukkan hukumomin gwamnati a duniya.

“Ba inda za ka je ka ɓoye kuɗin sata a duniya kuma ka yi tunanin ba za mu iya kamo ka ba”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan