Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Nasarar El-Rufa’i

195

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zama a Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar a zaɓen gwamna na 2019.

Jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar da ɗan takararta ma gwamna, Isa Ashiru sun garzaya kotun ne inda suke ƙalubalantar hukuncin da Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen da kuma ayyana gwamnan a matsayin wanda ya lashe zaɓe da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta yi.

To amma a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen, wadda tuni ta tabbatar da nasarar Gwamna El-Rufa’i, tana mai lura da cewa ɗan takarar na PDP bai gabatar da isassun hujjoji da zai iya tabbatar da iƙirarinsa ba.

Daga nan sai gungun alƙalai biyar na kotun suka tabbatar da matsayar Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen.

Majiyarmu ta ruwaito cewa gungun alƙalan biyar su ne UI Anyanwu, HAO Abiru, TY Hassan, BM Ugo da BB Aliyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan