Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranar Hutu

287

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Litinin, 11 ga Nuwamba, 2019 a matsayin ranar hutu don yin bukukuwan Maulidi don tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi).

Mohammed Manga, Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya taya al’ummar Musulmi murna bisa wannan rana kuma ya yi kira gare su da su koyi da koyarwar Annabin.

Ya ce koyi da halayen Annabi na soyayya, ƙarfafa gwiwa da juriya zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan.

Mista Aregbesola ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa kwanan nan Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da suke fuskantar ta; saboda haka, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karaya, kuma su zama masu mayar da hankali tare da manufa.

Ya bada tabbacin cewa da ɗimbin damammakin da ƙasar nan ke da su, ƙari da albarkatun al’umma da na ƙasa, nan ba da daɗewa ba Najeriya za ta shiga sahun ƙasashe da suka ci gaba.

“Da soyayya, jajircewa, sadaukar da kai, haƙuri da kishin ƙasa, babu shakka za mu gina babbar Najeriya”, in ji Mista Aregbesola.

Ministan ya bayyana ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da muhalli mai tsaro ga dukkan ‘yan Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan