Osinbajo Ya Tafi Nijar Don Halartar Taron ECOWAS

142

A ranar Juma’a ne Mataiamkin Shugaban Ƙasa zai halarci Taron Ƙolin Gaggawa na Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS a Jamuhoriyar Nijar.

Mai magana da yawun Mista Osinbajo, Laolu Akande, wanda ya bayyana haka a wani saƙon Twitter, ya ce za a yi Taron Ƙolin ne don tattauna harkokin siyasa a Guine Bissau.

Mista Akande ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasar zai bar Abuja ranar Juma’a da safe ya kuma dawo a ranar.

ECOWAS ta damu da yanayin siyasa da aka shiga a Guinea Bissau, wanda ya sa Shugaba José Mario Vaz na ƙasar ya yi wasu dokoki ranar 28 da 29 ga Oktoba, inda ya rusa gwamnatin ƙasar, ya kuma naɗa sabon Firayim Minista.

A ranar Laraba, Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a Guinea Bissau da su tabbatar an samu zaman lafiya, su kuma girmama umarnin Ƙungiyar Ƙasashen Afirka, AU da ECOWAS, kuma ya tabbatar da buƙatar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 24 ga Nuwamba kamar yadda aka tsara.

Da yake Allah-wadai da wannan mummunan al’amari, Kwamitin Tsaron ya yi kira ga dukkan ‘yan siyasa na ƙasar da su nuna dattako, su kuma hau teburin sulhu a matsayin hanyoyi kaɗai da za su iya warware bambance-bambancensu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan