‘Yan Najeriya A Ingila Sun Yi Zanga-Zanga Bisa Ziyarar Ƙashin Kai Ta Buhari

288

A ranar Alhamis ne ‘yan Najeriya ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da ziyarar ƙashin kai da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a Abuja House, Ingila, in ji jaridar SaharaReporters.

A cewar jaridar, Gabriel Agbontean ne ya jagoranci zanga-zangar.

Rahotonni sun ce masu ziyarar sun buƙaci cewa Shugaba Buhari ya dawo Najeriya ya gyara ɓangaren lafiya maimakon neman lafiya a ƙasashen ƙetare.

Sun bayyana cewa Shugaban yana kuma shirin shigo da likitoci daga ƙasashen waje zuwa Najeriya.

Sun nemi sanin bahasi me yasa Shugaban Ƙasar ke ci gaba da neman lafiya a ƙasashen waje a lokacin da gwamnatinsa ta hana shigo da kayayyakin da ake shigowa da su ƙasar kamar shinkafa.

Masu zanga-zangar suka ce tunda ziyarar Shugaba Buhari ta ƙashin kai ce, shi ne ya kamata ya biya dukkan kuɗaɗen da tafiyar tasa ke buƙata.

Dama an sha yin irin wannan zanga-zanga a Ingila a yayin ziyarce-ziyarcen ƙashin kai na Shugaba Buhari.

A lokacin da yake kamfe don zama shugaban ƙasa a 2015, ya yi wa ‘yan Najeriya alƙawarin cewa idan ya zama shugaban ƙasa, ba zai je asibiti a ƙasashen waje don a duba lafiyarsa ba, amma ya je Ingila ba sau ɗaya ba ba sau biyu a wa’adin mulkinsa na farko.

An yi hasashen cewa tun lokacin da ya hau karagar mulki, ya shafe kwanaki 200 a Ingila bisa dalilan rashin lafiya.

Kwanan nan ne ya hana ministoci yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje ba tare da ƙwararan dalilai ba.

Koda yake dai ba wani jami’in gwamnati da ya fito daga Abuja House don yi wa masu zanga-zangar jawabi, waɗanda suka tsaya a wajen fiye da sa’o’i biyu, an ga wasu mutane daga cikin gidan suna ɗaukar masu zanga-zangar a fim.

‘Yan sandan Birtaniya sun je wurin don tabbatar da cewa an yi zanga-zangar cikin lumana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan