Jan Hankali Zuwa Ga Malamai – Daga Aliyu Sani Madakin Gini

1092

Bayan sauraron hudubar limamin masallacin Annur(Wuse 2)da ke nan garin Abuja in da nayi sallar juma’a, nayi tunanin baiwa Malamai shawara akan abinda yashafi harkar mulki da siyasa.


Naji limamin wannan masallaci yayi magana akan Rufe Border da karin kudin haraji ga al’umar Nigeria cewar abune mai kyau. A fahmta ta, ko Mallam bai san abunda yake magana ba ko kuma ya buya da rigar addini yana kare ra’ayinsa na siyasa a mumbarin masallaci.

Maganar gaskiya bai kamata malamai su kau da kan su daga abinda ya dami al’umarsu ba saboda biyan bukarsu ga Gwamnati, al’umar Nigeria musamman talakawa suna cikin halin kunci da matsanancin talauci musamman mutanenmu na Arewa kuma kowa yasan wannan rufe Border da karin kudin haraji suna daga cikin abinda yakarawa talakawa wahalar rayuwa. Amma saboda bukatar kai tasa wasu malamai su ke goyon bayan haka.


Rufe Border nan ya jawowa yan kasuwarmu asara ta Billions of naira haka kuma karin kudin haraji ya jawo tsadar kayayyakin masarufi wanda sun kara jefa talaka cikin kuncin rayuwa amma saboda siyasa da tumasanci wai malamaine suke goyan bayan wannan tsari.

Ina jan hankalin malamai da suji tsoron Allah sukalli halin kunci da matsi da al’umar Annabi suke ciki su daina goyon bayan wannan rashin adalci, malamai akan kira ga addinin Allah da nasiha ga shugabanni aka san su ba banbadanci da tumasanci ga shugabanni ba.
Maganar gaskiya duk wanda yasan wani abu akan managing economy na kasa, yasan cewa ba’a kara haraji sanda ake fama da economic downturn domin in aka yi haka dole a samu tsananin rayuwa kamar yadda muke fama dashi yanzu.


Sannan wanna rufe border zai kara jawo matsala domin kasashe makotanmu sun fara daukar fansa.Yanzu maganar da ake kasar Ghana ta bawa duk dan NIgeria dake kasuwanci a kasar Ghana dasu rufe kantuna su komo gida Nigeria.


Maganar gaskiya abunda liman yayi huduba akai, ya bar tsarin fadakarwa ya koma siyasa da nuna goyan bayan gwabnatin tarayya akan karin kudin haraji da rufe border. Misalin da Mallam ya bayar da kasar Brazil bai yi daidai da abunda muke ciki anan NIgeria ba.


Ina bawa Malaman mu na addini shawara su guji shiga harkar siyasa domin yin haka zai zubar musu da kima da mutunci. Shiga harkar siyasa a wayance zai sa ayi musu radd, domin an gane ba domin Allah su ke yi ba ,a’a su na kare ra’ayin sune na siyasa Amma suna amfani da rigar addini.


Allah yasa nasihata ta amfanemu baki daya Allah yakawowa al’umar Nigeriya sauki yabamu mufita ta alheri.


Allah Ya nuna mana gaskiya ya bamu ikon bi,Ya nuna mana karya Ya bamu ikon kauce mata,Amin.
Bissalam
Aliyu Sani Madaki

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan