Jerin sunayen hadiman Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da Shugaba Muhammadu Buhari ya sallama daga aiki ya fito.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Laraba Labarai24 ta kawo rahoton cewa tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sallamar hadimai 35 daga aiki daga cikin hadimai 80 na Mista Osinbajo.
Majiyarmu ta ce hadiman da sallamar ta shafa, waɗanda aka ba su takardun ɗaukar aiki a Agusta, sun haɗa da wasu Manyan Mataiamka na Musamman, Mataimaka na Musamman da sauransu.
Sahihan majiyoyi waɗanda suka nemi a ɓoye sunayensu sun ce za a iya ba hadiman takardun sallama daga aiki a yau Laraba.
Tun kafin korar tasu, majiyarmu ta ce an tura hadiman zuwa wasu ma’aikatu da suka yi dai-dai da muƙamansu a watan da ya gabata. Ana zargin an yi haka ne don a hana su shiga Villa, Fadar Shugaban Ƙasa, a kuma rage tasirin Mataimakin Shugaban Ƙasa.
“Koda yake dai fiye da rabin hadiman suna karɓar albashi ne daga hukumomi masu bada tallafi, “shafaffu da mai” sun kore su don rage tasirin Mataimakin Shugaban Ƙasa”, a cewar wata majiya dake da masaniyar yadda al’amura ke gudana.
“Ba wanda aka tuhuma ko samu da wani kuskure. Ba magana ce ta rage kashe kuɗaɗe ba, saboda ba wani da aka kora daga Ofishin Shugaban Ƙasa ko kuma Ofishin Uwar Gidan Shugaban Ƙasa, inda aka naɗa ƙarin hadimai shida a cikin ƙasa da wata ɗaya da ya gabata. Kawai an sallame su ne don a rage tasirin Mataimakin Shugaban Ƙasa”, in ji majiyar.
Amma dai Fadar Shugaban Ƙasa, a wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a ta ƙaryata haka.
Ga jerin sunayen hadiman na Mista Osinbajo da Shugaba Buhari ya sallama:
- Jibola Ajayi – Mataimaki na Musamman, Shari’a
- Lanre Osinbona – Babban Mataimaki na Musamman, ICT
- Imeh Okon – Babban Mataimaki na Musamman, Kayayyakin More Rayuwa
- Jide Awolowo – Mataimaki na Musamman, Man Fetur da Gas
- Lilian Idiaghe- Mataimaki na Musamman, Bincike Shari’a da Bin Doka
- Umukoro – Mataimaki na Musamman, Naija Delta
- Bala Liman Mohammed – Babban Mataimaki na Musamman, Tattalin Arziƙi
- Edobor Iyamu – Babban Mataimaki na Musamman, Naija Delta
- Dolapo Bright – Babban Mataimaki na Musamman, Agro Allied Value Chain
- Toyosi Onaolapo- Mataimaki na Musamman, Aikin Gayya
- Gambo Manzo – Mataimaki na Musamman, Siyasa
- Bisi Ogungbemi – Mataimaki na Musamman, Al’amuran Siyasa
- Edirin Akemu – Babban Mataimaki na Musamman, Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari
- Akin Soetan – Babban Ƙwararren Mataimaki, Al’amuran Tattalin Arziƙi
- Aondaver Kuttuh – Ƙwararren Mataimaki, Bin Doka
- Ife Adebayo – Mataimaki na Musamman, Ƙirƙire-Ƙirƙire
- Yussuf Ali – Mataimaki na Musamman, Ƙa’idojin Mulki
- Tola Asekun – Babban Mataimaki na Musamman, Hukumar Kula da Kan Iyakoki ta Ƙasa
- Morakinyo Beckley – Mataimaki na Musamman, Off Grid Power
- Yosola Akinbi – Babban Mataimaki na Musamman, NEC
- Tochi Nwachukwu – Babban Mataimaki na Musamman, Cefanar da Wutar Lantarki
- Bode Gbore – Babban Mataimaki na Musamman, Siyasa
- Abdulrahman Baffa Yola— Mataimaki na Musamman, Siyasa
- Kolade Sofola – Mataimaki na Musamman, Kayayyakin More Rayuwa
- Ebi Awosika – Babban Ƙwararren Babban Mataimaki, Aikin Gaya
- Muyiwa Abiodun – Babban Mataimaki na Musamman, Wutar Lantarki
- Forri Samson Banu –Mataimaki na Musamman, Sana’o’i
- Bege Bala – Mataimaki na Musamman, BPE
- Feyishayo Aina – Babban Mataimaki na Musamman, Aikin Gayya
- Halima Bawa— Mataimakiya ta Musamman, Aikin Gayya
- Nkechi Chukwueke – Mataimaki na Musamman, Aikin Gayya
- Ilsa Essien – Mataimaki na Musamman, Kafafen Watsa Labarai