Mansur Ahmed hadimi na musamman akan harkokin kafafen sadarwa na zamani ga tsohon gwamnan jihar Jigawa,l Sule Lamido, ya bayyana wasu matsaloli da su ka zama ruwan dare a tsakankanin al’ummar yankin arewcin kasar nan.
Mansur Ahmed ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk, in da ya zayyano miyagun halaye guda a shirin (20) da su ka zamewa al’ummar arewcin Najeriya matsala. Halayen da ya zayyano sun hada da:

- K’abilanci da ci da addini don biyan bukata
- K’iyayyar siyasa
3 Son kai da k’wadayi - Sace-sace da fashi da makami
- Garkuwa da mutane
- K’age da fallasa da yad’a karya akan jama’a
- Kisan gilla da b’arnar dukiya
- Cin mutunci da yiwa juna k’azafi
- Cin hanci da girman kai
- Rashin adalci da son zuciyar shugabanni
- Haddasa fitina da tashin hankali
- Shaye-shayen kw’ayoyi ga mata da maza
- Yawan marasa aikin yi
- Talauci da zaman kashe wando
- Rashin alk’ibla da makoma ga matasa.
- Rashin girmama manya da dattawa
- Nuna halin ko’in kula akan damuwa ko annobar da bata shafe ka ba.
- Yin dokoki da zasu musgunawa talaka
- Rashin yiwa iyaye biyayya.
- Shugabanni mak’aryata, mayaudara, mazambata.
Meye abin yi?
Turawa Abokai