Na Yi Matukar Takaici Da Furucin Sarkin Kano Sanusi II – Nasiru Zango

2281

Tare da dukkan girmamawa nake bayyana matukar takaici da kalaman da nake ji cewar sun fito ne daga bakin Mai martabar sarkin Kano, gaskiya idan har gaskiya ne kalaman sun yi tsauri Bai kuma dace mu jiyo su daga bakin jagoran mu ba.

Magana ce ta cewar ya kamata a hukunta iyayen yaran nan 9 da aka sace. To meye laifin su?


Da yawa daga cikin yaran fa an sace su ne akan hanyar zuwa makarantar islamiyya, Kuma dukkan su yayan talakawa ne, wadanda basu da ikon daukar dogari domin yiwa yayansu rakiya, Kuma gashi ance a saka Yara a makaranta.


Wasu daga ciki an shiga har cikin gida ne aka sace yaran Bayan an faki idon iyayen su.


To Amma koma wacce hanya aka bi aka sace su da wanne zamu ji? Yanzu fa da yawa daga cikin yaran an sace su tsahon shekaru, an sauya musu suna da addini, Kuma Bayan tsahon lokaci da suka dauka cikin halin kunci na rashin tabbas, da yawa daga cikin su yanzu sun kasa komawa daidai, ibadun addinin mu yana musu wuya, ana ta Fama wajen kokarin mayar dasu Kan hanya, Bayan cutar da akayi mana wajen sauya musu tunani.


Kamata yayi jagororin mu su mayar da hankali wajen yi mana dannar kirji ba kirarin a kama iyayen yaran da laifin sakaci ba.

Ina roko ga shugabannin mu su Kara zage damtse wajen kare martabar mu da kiyaye mutumcin mu, kamar yadda jagororin wadannan barayin suke yi. Hatta jaridun su basa Yada gazawarsu komai kankantar ta, domin hatta wannan labari na satar da suka yi jaridunsu shiru suka yi saboda ba yayan bora ne suka yi laifin ba. Allah ya taimaki al’ummar mu ya kare mu ya Kara hada Kan mu amin.

Turawa Abokai

3 Sako

  1. Abin takaici abin bakin ciki nama najan kare maimakon kare yaja nama masarautar Kano idan bazata iya yiwa iyayen yarannan adalcin daakasan masarautar dashiba to baikamata takunsa musu takaiciba Allah Muna rokonka kada ka kamamu dalaifin wawayen cikinmu

  2. Lallai naji wannan batu da’ake alaqantashi da mai martaba kuma in har hakan ya tabbata gaskiya ne to lallai akwai babban-gibi tsakanin shuwagabanninmu da kuma mu da ake mulka . Girman wannan magana yawuce duk-yadda ake tunani kuma dukkan metunanin cewar iyayen yaran yakamata a hukuntasu to kamata yayi afara hukunta su mahukuntanmu Wanda halin tsaron mu da lafiyarmu , da jin dadinmu ya rataya ne awiyansu , bugu da qari mu muna ganin cewar kamata yayi ace mahukuntan mu sun dauki ragamar kulawa da wa’innan yara , ta hanyar ware musu kwararru da za su dinga kulawa da su Dan ganin dukkan al’amuransu sun dawo dai-dai wato ina nufin Councilling , ta hanyar tarbiya , addini , harshe , sakamakon haryanzu wasu daga cikin yaran nan fa basa majin Hausa balle kuma kayi tunanin zasuyi kokuma zasu’iya yin ibada kamar yadda shara’a ta shar’anta , muna kira da gwamnati da tasake lale , ta kuma kar6o yaran-nan a hannun iyayensu , kana ta killace su qarqashin kulawar gwamnati acigaba da basu kulawa ta musamman domin ganin sun dawo haiyacinsu kafin daga bisani kuma amiqasu ga iyayensu … Muna ji muna gani abun da yafaru a south Africa , wa’inda suka dawo gida komuma suke kokoqarin dawowa a wanchen lokacin qarqashin shirin gwamnati da tayi musu tayin su dawo gida , Wanda wani kampanin jigilar jiragen saman mallakal wani dan’najeriya ya jagoranci wannan aiki bisa ra’ayinkai Wanda wannan ba qaramar gudu mawa bace , sai da hukumar nan ta Nigerian diaspora Commission , ta dauki ragamar kulawa da su dakuma basu kulawa ta musamman da ma koya musu sana’oi bugu daqari bayan sana’oin ma har da tallafi da akayi alqawsrin za’abasu wai dai da zimmar , tallafa musu sakamakon sun-dade basa kasar kuma yanayi , yazo da sunbar dayawan abubuwansu awaccen kasa , wasu ma sun-rasa dukiyoyinsu , kuma mahukunta suna son insun dawo gida najeriya kada su rasa abunyi … Wannan yasa mahukunta sukaiyi musu wannan tsari , menene lefi in mun yi wa wadannan yaran namu irin wannan tanadi ?

    Lallai muna jawo hankalin mahukunta da su dinga tsare-tsaren da zai shafi kowannan 6angare wannan shine zai taimaka wajen cigaba da zama qasa Daya al’uma Daya . Yakamata Mahukuntanmu na jahar kano da attajiranmu su hada hannu wajen ganin yarannan sun samu kulawa ta musamman amai-maikon ace an danganasu da iyayensu adai dai lokacin da suke da buqatar kulawar kwararru ta fannoni da dama ! (SMB)

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan