Mara Lafiya Da Ya Nemi Tallafin Miliyan 15 Don Yi Masa Dashen Ƙoda Ya Rasu

307

Mara lafiyar nan mai cutar ƙoda, Mahmud Aminu Daneji, wanda ya nemi tallafin miliyan 15 don yi masa dashen ƙoda a Indiya ya rasu.

Mista Daneji, wanda aka fi sani da Mamuda Elder ya rasu ne ranar Lahadi yana da shekara 46, ya bar mace ɗaya da ɗa ɗaya.

Ya rasu yayinda yake neman tallafin miliyan 15 don ba shi damar tafiya Indiya don yi masa dashen ƙoda.

A ranar Litinin ɗin nan da safe za a yi jana’izarsa a Layin Bata dake unguwar Gadon Ƙaya a cikin birnin Kano.

A wata tattaunawa da ya aka yi da shi kwanan nan, ya faɗa wa jaridar Kano Focus cewa a shekarar 2001 ne ƙodojinsa biyu suka daina aiki bayan ya gamu da hawan jini.

“Mutum ne ni mai lafiya da kuzari kafin hawan jini ya kwantar da ni. Ina rayuwata dai-dai kafin jinina ya hau zuwa 220 a watan Maris, 2001”, ya tuna haka.

A watan Oktoba, 2006, an yi wa Mista Daneji dashen ƙoda cikin nasara, inda ya samu lafiya tsawon shekaru huɗu kafin ta ƙara tsayawa a 2010.

Ya bayyana cewa daga 2001, an yi masa wankin ƙoda sau 1,473.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Sharhi: Ba shakka muna amfana da Labarai 24 da labarai da dumi-duminsu. Muna godiya kwarai da gaske. Allah ya kara jagoranci.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan