Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Saudiyya, ta bayar da shawarar gaggauta yin wata sabuwar doka da za ta haramta yi wa ‘yan matan da ba su kai shekara 18 ba aure.
Jaridar intanet ta Saudi Gazette ta rawaito cewa a wata sanarwa, hukumar ta nuna cewa duk yarinyar da ba ta kai shekara 18 ba to ba ta mallakin hankalinta ba a saboda haka ba ta isa aure ba.
Sanarwar ta nuna cewa yi wa yarinyar da ba ta kai shekara 18 aure ba ya saba da dokokin kasar ta Saudiyya masu yin kariya ga kananan yara da hana ci musu zarafi da safarar su.
Hukumar ta kare ‘yancin dan adam ta Saudiyya ta ce “sidirar farko ta dokokin kare ‘yancin yara na duniya wadanda masarautar saudiyya take bi sau da kafa, sun ce duk mutumin da bai kai shekara 18 ba to ana daukar shi a matsayin karamin yaro ko yarinya.
Hukumar ta yi bayani dangane da irin ‘illolin’ da ake samu sakamakon auren wuri da ake yi wa kananan yara, inda ta ce ta yi wani nazari tare da wasu kungiyoyi.
Ta ce “auren wuri na yi wa yara mata illa a tunaninsu da yanayin jikinsu.”
Yi wa dokar hana yi wa wadanda ba su kai shekara 18 aure ba in ji hukumar zai taimaka gaya wajen bai wa yaran kariya sannan kuma zai sa a rinka samun zaman lafiya tsakanin ma’aurata.


[…] Muƙalar Da Ta GabataKasar Saudiyya Na Yunkurin Yin Dokar Hana Aurar Da Mata Yan Kasa Da 18 […]