Masoya Annabi Ne Kadai Su Ke Yin Maulidi- Sheik Dahiru Bauchi

621

Wani bangare na al’ummar Musulmin duniya na gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallam, abin da ya sa aka bai wa ma’aikata hutu a fadin kasar nan.


An haifi Annabi Muhammad a ranar 12 ga watan Rabi Awwal mafi rinjayen kauli, wanda shi ne wata na uku daga cikin jerin watannin Musulunci guda 12.


Malaman tarihin Musulunci sun ce, an yi wa shekarar haihuwar Annabi lakabi da shekarar giwaye saboda yadda Allah ya hallaka rundunar Sarki Abraha al-Ashram na Yemen wadda ta shigo garin Makka da nufin rushe Ka’aba.


Malaman tarihin sun ce, rundunar ta Sarki Abraha ta yi amfani da giwaye da nufin kaddamar da farmaki kan Ka’aba amma Allah ya aiko tsuntsaye dauke da tsakwankwani da suka hallaka daukacin mayakan na Yemen saboda karramawa ga Annabi Muhammadu Sallahu Alihi Wasallam wanda aka haifa a wannan shekarar.


A yayin zanta wa da manema labarai, Sheik Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa, watan Rabi’u Awwal ya samu daraja ne saboda a cikinsa ne aka haifi Manzan Allah.
Babban Malamin ya kara da cewa, “masoya Annabi da ke damuwa da shi, su suke yin a Maulidi”.

Sai dai wani bangare na Malaman addinin Islama na cewa, Maulidi wani al’amari ne da ya saba da sunnah ko kuma koyarwar Manzan Allah, abin da ya sa suke ganin bai halatta a gudanar da shi ba.


Malaman sun kafa hujjar cewa, Manzan Allah da Sahabbansa ba su yi bikin Maulidi ba saboda haka ba shi da asali a Musulunci.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan