An Gurfanar Da Ma’aikatan Kotun Musulunci Bisa Zargin Sata

249

Ranar Alhamis ne ake sa ran wata babbar kotu a birnin Kano za ta fara shari’ar wasu mutane wadanda ake zargi da “sace” kudin wani bawan Allah mai suna Sanusi Yakubu.

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arziki Ta’annati ta kasa wato EFFC, ita ta kai mutanen, wadanda ma’aikatan wata kotun Musulunci ne, gaban kuliya.

Tana tuhumar su ne da hada baki da wani ma’aikacin banki su kwashe kudin da ke asusun ajiyar Malam Sanusi.

A wata sanarwa da ta fitar, EFCC ta ce Sanusi Yakubu ya kawo mata korafi yana zargin cewa: “Wani mutum mai suna Williams Aondo (wanda tuni ya mutu) da ke aiki a wani banki ya hada baki da mutanen biyu sun shigar da magana a gaban wata kotu suna ikirarin cewa ya mutu.

“Sun yi hakan ne bayan da suka lura cewa an kwashe shekaru ba a taba asusun ajiyarsa na banki ba, ba su san cewa yana raye a Saudi Arebiya ba”.

Kotun shari’ar musulunci, wadda aka kai batun gabanta a wancan lokaci, ta dogara da bayanan da ma’aikatan nata suka gabatar mata, kuma ta bayar da umarnin a rufe asusun ajiyar Malam Sanusin.

Haka zalika ta nemi a kai mata kudin da ke cikin asusun har naira miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin da biyar da naira dari bakwai da ashirin da takwas, don raba wa magada.

Wadanda ake karar dai sun musanta laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan