‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda 3 A Kaduna

204

A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga da ba san ko su wane ne ba suka harbe ‘yan sanda uku har lahira a ƙaramar hukumar Sanga dake jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun harbe ‘yan sandan uku ne a wani wajen binciken ababen hawa tsakanin Fadan Karshi da ƙauyen Sabon Gida.

Abubakar Abba, Mataimakin Shugaban ƙaramar hukumar Sanga ya tabbatar da faruwar al’amarin ga manema labarai ranar Laraba.

Ya ƙara da cewa tuni an kawo gawarwakin ‘yan sandan Babban Asibitin Gwantu.

“‘Yan sanda biyu sun mutu nan take, na ukun kuma ya mutu a kan hanyar zuwa asibiti”.

“Tuni jami’an sun tashi tsaye don fara bincike, yayinda aka yi kira ga al’ummar garin da su kwantar da hankalinsu”, in ji shi.

Ya nuna rashin jin daɗi bisa yawaitar aikata laifuka a yankin, sannan ya yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su tashi tsaye don fuskantar wannan ƙalubale.

Mataimakin Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Suleiman Abubakar, shi ma ya tabbatar da afkuwar al’amarin.

Ya ce nan ba da daɗewa ba za a fitar da sanarwa game da wannan al’amari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan