Kano Ta Samu Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda

403

Babban Sifeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP, Mohammed Adamu, ya turo Habu Sani Ahmadu a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP, na Jihar Kano.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Mista Ahmadu zai maye gurbin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano mai ci, Ahmed Iliyasu, wanda aka ciyar da shi gaba zuwa muƙamin Mataimakin Sifeto Janar, AIG, mai kula da Shiyya ta 2 a jihar Legas.

A cewar wata sanarwa da Frank Mba, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa ya fitar, akwai sauran sabbin Kwamishinonin ‘Yan Sandan da aka tura sauran jihohi da suka haɗa da:

CP Nkereuwem A. Akpan, jihar Kuros Ribas
CP Kenneth Ebrimson, jihar Akwa Ibom
CP Imohimi Edgal, jihar Ogun
CP Habu Sani Ahmadu, jihar Kano
CP Lawal Jimeta, jihar Edo State
CP Philip Sule Maku, jihar Bauchi
CP Odumosu H. Olesegun, jihar Legas.

Mista Mba, wanda Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ne, ya ce waɗannan muƙamai za su fara aiki ne nan take.

“Babban Sifeton ‘Yan Sanda yana kira ga sabbin jami’an da aka tura da su tabbatar da ci gaba da bunƙasa nasarorin da waɗanda suka gada suka samu ta fannin kare al’umma da da yaƙi da laifuka.

“Yana kuma umartar sabbin Kwamishinonin ‘Yan Sandan da su yi aiki da masu ruwa da tsaki wajen ɗaukar matakai na ba sani ba sabo da kuma matakan ko-ta-kwana da al’umma suka amince wajen hana aikata laifuka a yankunan da aka tura su.

“Bugu da ƙari, Babban Sifeton ‘Yan Sandan yana kira ga al’ummar jihohin da abin ya shafa da su ba sabbin Kwamishinonin ‘Yan Sandan haɗin kan da ya dace don tabbatar da yin nasarar su a wajen sauke nauyin dake aka ɗora musu”, in ji Mista Mba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan