Zaɓen Kogi: Ma’aikatan INEC 30 Sun Yi Ɓatan Dabo

267

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ma’aikatanta na wucin gadi guda 30 sun yi ɓatan dabo a zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar a jihar Kogi.

Ma’aikatan wucin gadin sun yi aiki ne a ƙaramar Olamaboro.

INEC ta bayyana ɓatan ma’aikatan ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 1:00 na dare a yayin tattara sakamakon zaɓe na ƙarshe a ƙaramar.

Ma’aikatan na INEC da suka ɓata sun haɗa da Turawan Zaɓe, POs, da Mataimaka Turawan Zaɓe, APOs, na tashoshin zaɓe na Imane mazaɓa ta 1 da ta 2 na ƙaramar hukumar ta Olamaboro.

Da yawa daga cikin ma’aikatan wucin gadin na INEC matasa ne masu yi wa ƙasa hidima.

Kamar yadda aka rasa inda jami’an suke, sakamakon tashoshin zaɓen da suka yi aiki shi ma ya ɓata.

Da yake sanar da ɓatan ma’aikatan, Baturen Zaɓe na ƙaramar hukumar Olamaboro mai kula da tattarawa da sanar da sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar, Garba Mahmood, ya ce an samu rahotan ɓatan ma’aikatan wucin gadin ne bayan da wasu ‘yan sanda suka lura cewa an yi musu ganin ƙarshe ne jim kaɗan bayan kammala zaɓe da ƙarfe 2:00 na ranar a ranar Asabar.
Mista Mahmood ya ce an yi ta kiran wayoyinsu amma ba su shiga ba.

Ba a iya samun Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kogi ba don jin ta bakinsa game da matsayin ɓatan ma’aikatan.

Zaɓen gwamnan da aka gudanar yana cike da tashe-tashen hankula, sace akwatinan zaɓe, tsorata masu zaɓe da siyan ƙuri’u a sassa da yawa na jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan