KAROTA Za Ta Rage Yawan Baburan A Daidaita Sahu A Kano

355

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta sanar da shirinta na rage yawan baburan A Daidaita Sahu a Kano.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Manajan Darkatan KAROTA, Bappa Babba Dan-Agundi, ya bayyana hak ranar Litinin yayin kare kasafin kuɗin hukumar a zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Mista Dan-Agundi ya ce KAROTA za ta shigo da wani sabon tsarin yin rijista wanda zai rage yawan baburan masu ƙafa uku na A Daidaita Sahu daga 500,000 zuwa 200,000.

Ya kuma ce KAROTA za ta kafa na’urar tsaro a kan baburan A Daidaita Sahu masu rijista a dukkan faɗin jihar Kano.

“Matakin fara kafa na’urorin a kan baburan masu ƙafa uku ya biyo matakin da gwamnatin jihar ta yanke na ƙyale direbobin baburan su ji gaba da sana’arsu.

“Saboda haka, ya zama wajibi a gare mu mu fara kafa na’urorin, waɗanda ke da manufar kula da ayyukansu a dukkan faɗin jihar”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa KAROTA tana son samun kuɗin shiga N6000,000,000 a shekarar 2020 ta hanyar yin rijista da karɓar tara daga hannun masu karya dokar tuƙi.

Mista Dan-Agundi ya ce KAROTA za ta shigo da aikin gayya a matsayin hukunci ga masu take dokokin tuƙi, saboda manufarta ba shi ne tara kuɗin shiga ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan