Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Zai Koma Jam’iyyar APC

2085

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, na shirye-shiryen komawa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Wani mai suna Anyali Pius kuma jigo a jam’iyyar PDP wacce ta fadi zaben gwamnan jihar Bayelsa ne ya wallafa wannan labari, inda yace “A zaben gwamnan jihar Bayelsa da ya gabata ranar Asabar din nan, hatta matar tsohon shugaban kasa, Patient Jonathan, ta yiwa dan takarar jam’iyyar APC kamfen.

“Kuma Jonathan bai yi Douye Diri ba, saboda Douye ya yaki Jonathan da Timi Aleibe a siyasa Wanda kuma sune suka rene shi” Inji Pius


Majiya Gidan Radiyon Vision, Abuja

Turawa Abokai

3 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan