Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya lashi takobin samar da banɗakunan tafi-da-gidanka da ƙarin ɓanɗakunan gwamnati a jihar don yaƙar ɗabi’ar bahaya a fili.
Kwamishinan Muhalli, Kabir Getso, ya bayyana haka ranar Talata a Kano yayinda yake yi wa manema labarai jawabi a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Ranar Banɗaki ta Duniya.
Mista Getso ya ce Gwamna Ganduje ya nuna damuwa bisa yawaitar yin bahaya a fili a jihar Kano, ya kuma yi kira da a samu dabarun kawar da za a kawar da haka.
Ya ce gwamnatin jiha a shirye take wajen kawo ƙarshen ɗabi’ar bahaya a fili kamar yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ayyana dokar ta-ɓaci a kan ruwa, tsaftar muhalli da kiwon lafiya, wato WASH, a ƙasar nan.
Kwamishinan ya ce gwamnati za ta samar da banɗakunan tafi-da-gidanka da banɗakunan gwamnati a muhimman wurare musamman a wuraren da ake da mutanen da ba su da gida.
Ya lura da cewa yin bahaya a fili yana haifar da cututtukan da ake ɗauka ta iska, ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da ɗaidaikun mutane da su taka rawar da ta dace wajen kawo ƙarshen wannan mummunar ɗabi’a.
“Banɗaki ba kawai banɗaki ba ne, amma abu ne mai tseratar da rayuwa, mai kare mutunci kuma mai bada dama. Ko waye mutum, ko daga ina yake, tsaftar muhalli haƙƙinka ne”, in ji Mista Getso.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya bada rahoton cewa jihar Kano ta bi sahun kamfen da ake yi a duniya na hana ɗabi’ar yin bahaya a fili ta hanyar ɗaukar kamfen ɗin zuwa tashoshin motoci da kuma yankunan da suka shahara da yin bahaya a fili.
Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware ranar 19 ga watan Nuwamba na kowace shekara a matsayin Ranar Banɗaki ta Duniya don wayar da kai bisa haƙkin da ɗaiɗaikun mutane ke da shi na samun banɗakuna.
[…] Da Ta GabataGanduje Ya Lashi Takobin Yaƙar Ɗabi’ar Yin Bahaya A Fili Muƙala Ta GabaShekaru 62 Na Tsohon Shugaban Kasa Jonathan: Me Ka Sani Game Da […]