Gwamnatin Tarayya Ta Ware Fiye Da Biliyan N4 Don Sake Gina Hanyar Kano-Gwarzo-Dayi

362

Gwamnatin Tarayya ta ware fiye da naira biliyan N4 domin sake gina hanyar Kano-Gwarzo-Dayi, wadda aka yi watsi da ita tsawon lokaci.

Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin-Maliya, wanda ya bayyana haka ga jaridar The Nation ranar Lahadi a Kano, ya bayyana damuwa bisa halin da hanyar ke ciki, wadda ta haɗa Kano da jihohin Katsina, Sokoto, Zamfara da Kebbi da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.

Sanata Jibrin-Maliya, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattijai, ya ce an kammala dukkan shirye-shirye don fara aikin sake gina hanyar mai tsawon kilomita 70 cikin gaggawa, inda da farko za a saki naira biliyan N2.

A ta bakinsa: “Na daɗe ina tattaunawa da Gwamnatin Tarayya bisa mummunan halin da wannan hanya mai muhimmanci ke ciki”, yana mai ƙarawa da cewa, “a watannin huɗun farko na 2020, za a bada kwangilar aikin”.

Ya ce ƙudirin aikin hanyar yana gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa, saboda haka, za a samar da naira biliyan N2 don bada kwangilar.

Ya ce hanyar, wadda an yi watsi da ita tsawon lokaci, idan aka kammala aikinta za ta bunƙasa harkokin zamantakewa da na tattalin arziƙi a tsakanin al’ummomin dake zaune a kan hanyar, da ma na jihohin da suke haɗe da jihar Kano.

Hanyar, wadda ba ta samu wata babbar kwaskwarima ba tunda Shugaban Mulkin Soja, Janaral Ibrahim Babangida ya gina ta, idan aka kammala aikinta, za a samu raguwar haɗura da ake samu a kanta kullum.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan