Abubuwan Da Su Ke Kawo Mutuwar Aure – Aliyu Dahiru Aliyu

413
  1. Binciken masana ya nuna cewa wanda ya yi aure musamman saboda siffa (kyau) to aurensa na da yiwuwar lalacewa saboda bayan zama zuwa wani lokaci ma’aurata suna dena ganin kyan abokan zamansu. Sai dai na waje ya ce matar wane kyakkyawa ce amma shi dena gani zai yi. Ka lura ko yan gidanku baka fiye ganin kyansu ba sai dai na waje ya gani? Sabo da gani yana cire kyan da aka saba gani.
  2. Wanda ya yi aure saboda “sex” shi ma zai zama “disappointed” daga karshe saboda mafi yawan yadda mutane suke tunanin “sex” ba ya kaiwa haka. Na san mata da yawa da suka ce “sex is overrated” don haka auren ma ba wani dadinsa suke ji ba saboda tun asali tunanin da suke yi masa ya banbanta da yadda suka sameshi. “Sex” yana da muhimmanci a aure musamman ta fuskar maza amma ba shi ne babban ginshiki a ciki ba.
  3. Wanda ya auri mara mutunci yana tunanin bayan aure za ta nutsu shi ma ya nemowa kansa jafa’i ne. Mafi yawan halayyoyi ana boyesu kafin aure sai bayan aure a bayyanasu. Kada ka taba dauka za ka iya mayar da amalanke to koma mota. Tsarin shi ne mutunci ko hali mai kyau daga waje ake fara ganeshi tun ana boye rashin mutunci. Mafi yawa an fi komawa marasa mutunci bayan aure.
  4. Wanda ya boye aibukansa sai bayan aure matarsa ta gano shi ma ya kunnawa kansa bala’i. Ka fadi gaskiya tun kafin aure domin a so ka a yadda kake. Tsoron rabuwa da budurwarka zai iya janyowa silar rabuwar aurenku bayan ta shigo. In dai aure kake so ya tsaya to ka fadi gaskiya ko da kana tsoronta.
  5. Masana sun bayyana cewa mafi yawa daga karshe abokantaka ita take rike aure ba soyayya irin ta saurayi da budurwa ba. Wanda ya tashi da iyayensa zai iya lura sun fi hira kamar abokai ba wai irin yadda yake zuwa gun budurwarsa ba. To ya zama tun kuna soyayya ka mayar da budurwarka abokiyarka domin abokantaka (kauna) ta fi dadar da aure fiye da gwalangwason da ake na soyayya.
  6. Ka karanta litattafai da yawa da suke magana akan aure da zamantakewarsa domin littafi yana tattara abin da wasu suka fahimta cikin dadewar lokaci ne. Ba lallai ka samu komai a littafi ba amma tabbas za ka rage abubuwa da yawa, musamman matsalolin da kowa yake shiga. Ka yi karatu sosai domin da akwai sirrin da Allah ya ce da Annabi ya yi karatu duk da ya san ba mai karatun ba ne.

Wannan shawara ce ba wai cewa na yi sai kowa ya dauka ba. Don na san wasu ko mai za ka gaya musu ba za su yarda ba. Wanda duk zai auri “fara ko da mayya ce” shi ta shafa don ba ni zan shiga bakin ciki ba. Ni dai nawa na fadi abin da na sani.

Aliyu Dahiru Aliyu Jami’i a kungiyar cigaban demokaradiyya, da ke Abuja.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan