Ana Aurenmu Ne Kawai Domin A Ji Dadin Saduwa – Jaruma Fati K. K

5413

A wata hira da aka yi da tsohuwar jaruma Fati KK ta bayyana cewa abinda maza ke bukata a jikin mace mai kyau irinta shi ne su aureta su gama jin dadinta su sake ta

Ta ce yanzu ita tsoron sake yin aure take yi, saboda tana kallon maza duka halinsu daya ne

Ta bayyana cewa ta fito daga wajen iyaye da suke da fahimta ga kuma ni’ima ta addinin Muslunci ita ce ta saka kullum take yiwa Allah godiya

Fati KK tsohuwar ‘yar wasan fina-finan Hausa ce ta Kannywood wacce bata bukatar doguwar gabatarwa game da ko wacece saboda sunan da tayi lokacin da take masana’antar. ‘Yar asalin garin Kontagora ce dake jihar Neja.


A lokacin da tauraruwar Fati ke haskawa kawai sai aka nemeta aka rasa abinda yasa masoyanta wasi-wasin in da ta shiga.


A wannan hirar da ta yi da Aliyu Askira wakilin jaridar Blueprint, ta yi bayani akan auren, da kuma dawowar ta harkar fina-finan Hausa.


Jaridar Blueprint: Menene sirrin wannan kyau din da kika kara?
Fati KK: Farko dai zan iya cewa ina farin ciki na samun iyaye wadanda suke da fahimtar rayuwa, da kuma addinin Musulunci, addinin da yake nuna mana cewa duk abinda ya faru da kai ka dauke shi a matsayin kaddara.

Daga : Jaridar Blueprint

Turawa Abokai

3 Sako

  1. Ni mai magana Baban Zarah ina kira da fati keke data gaggauta janye wannan kalamai datayi sakamakon ita musulmace ba’a sammu da wannan furuciba. Hakuri da godiyan Allah shine aran mutum mumini sannan kuma ina da tambaya zuwa ga fati keke? 1. Cewa auren da kikayi na farko bakiji dadi ba shine yasa ki fadan haka. 2. Shikenan ki gama aure a duniya. 3. Ina matsayin sha’awan da kike dashi. 4. Menene matsayin komawa film naki duk da ana zargi kannywood yanzu da lalata mata. 5. Shin kin hakura da aure kenan a duniya. 6. kincire ran samu miji nagarikenan a gaba??? Don Allah ina jiran wanna Amsa a wajen Jaruma fati keke. Kisani ni masoyin kallon finafinakine. Nagode By: Baban Zarah.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan