Kiwo shi ne aikin da ya kunshi rainon dabbobi da tsuntsaye domin cin gajiyarsu ko amfana daga garesu, ta hanyar amfani da abinda suke samarwa kamar nama, gashi, mai, nono, kashi, kwai da dai sauransu.
Kiwo ya hada da kula da dabbobi ko neman karin yawansu dan saidawa da basu abinci, da basu magani. A duk fadin duniya al’ummomi daban-daban nada ire-iren hanyoyin da suke kiwata dabbobinsu kuma ya banbanta da na wasu al’ummar, haka zalika mafiya yawan dabbobin da aka fi kiwota su a duniya sune dabbobi kamar; Saniya, Tumaki, Akuya, Kaji, Agwagwi, Kifaye da sauransu.
Agwagwa na daya daga cikin tsuntsayen gida da akan same su a wasu daga cikin gidajen Hausawa da aka tanadesu domin yin kiwonsu domin nama ko samun kudi.
Amma saboda yanayin sauyin zamani da ke samu yau da kullum, hakan ya sanya kullum ake samun koma bayan ko kuma karancin irin Agwagwa a cikin al’ummar wannan zamani, musamman a kasar Hausa.
Tun asali wasu mutanen ba sa son kiwon agwagi kamar yadda su ke son kiwon Kaji, bisa dalilin yadda su ke da kazanta a lokacin kiwonsu. A ko ina agwagwi suna bukatar ruwa wanda idan aka rashin sa’a sai kare wajen yin amfani da kwata da saurare guraren da ya ke tara ruwa.
Duk da cewa yankunan karkara su na da albarkar fadamu tare da kududdufai, amma ko a can abu ne mai wahala a samu in da ake kiwon agwagwi kamar a shekaraun baya. Abin tambayar a nan shi ne me ya jawo hakan?
