Melaye Ya Gabatar Da Hujjojin Maguɗin Zaɓe A Ofishin INEC, Ya Buƙaci A Soke Zaɓe

221

A ranar Laraba ne tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, kuma tsohon shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai Mai Kula da Birnin Tarayya, Abuja, Dino Melaye ya yi dirar mikiya a ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, inda ya buƙaci a soke zaɓe a Mazaɓar Sanata ta Kogi ta Yamma.

Mista Melaye ya samu tarba daga Sakataren INEC, Rose Orianran-Anthony da kuma Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Zaɓe, Festus Okoye.

Mista Melaye ya je ofishin da faya-fayan bidiyo 21 dake ƙunshe da yadda wakilan gwamnatin da ake zargin sun yi harbe-harbe, sannan ya faɗa wa manema labarai cewa ƙoƙarinsa na ƙwato haƙkinsa “yaƙi ne da ba gudu ba ja da baya, babu miƙa wuya”.

Ƙorafin na Mista Melaye, mai ɗauke da kwanan watan 18 ga watan Nuwamba, 2019, da taken: “Kiran Soke Zaɓen Mazaɓar Sanata ta Kogi ta Yamma A Wasu Yankuna Da Aka Gudanar Ranar 16 Ga Nuwamba, 2019”, lauyansa, Tobechukwu Nweke ne ya gabatar da shi.

Wani ɓangare na ƙorafin yana cewa: “Daga ƙarshe, duba da waɗannan tashe-tashen hankula da aka ambata a sama, harbe-harben bindiga da kashe-kashe, tarwatsa zaɓe, sace akwatinan zaɓe, dangwale fiye da sau ɗaya, laifukan zaɓe da dama, rashin bin ƙa’idoji da kuma yin ƙafar angulu ga tsarin gudanar da zaɓe da aka yi a dukkan ƙananan hukumomi bakwai a jihar Kogi waɗanda aka nuna a cikin faya-fayan bidiyo da aka kawo a nan, da kuma hujjoji a sakin layuka na 1-5 a sama waɗanda suka nuna cewa ba a yi zaɓe ba a Mazaɓar Sanata ta Kogi ta Yamma, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2010 (wadda aka yi wa kwaskwarima) ta tanada, da kuma ƙa’idoji da dokokin da aka bayar don yin zaɓen, muna kira ga hukumar da ta soke zaɓen Sanatan Kogi ta Yamma gaba ɗaya da aka yi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019”.

Mista Okoye, wanda ya karɓi ƙorafin a madadin Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce hukumar za ta duba ƙorafin, kuma za ta ɗauki matakin da ya wajaba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan