Ranar Talabijin Ta Duniya: Ya Tasirinta Ya Ke A Rayuwar Dan Adam?

166

Ranar 21, ga watan Nuwamba rana ce da Majalisar Dinki Duniya ta ware domin bikin ranar Talabijin a duniya.


A wannan rana ana duba irin ayyukan da gidajen talabin ke bayarwa ga alumma , da kuma jan hankalin gwamnatoci wajen tallafawa, da bunkasa gidajen talabijin.

Rahotanni sun nuna cewa ana samun karuwar masu kallon Talabijin a kasashe masu tasowa, abinda aka sani da kasashe da suka cigaba.


A shekarar 1996, ne dai babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da wannan rana domin duba rawar da Tala.


Tasirin Talabijin ga dan Adam, shi ne yadda take mika sako ga jama’a da ake ji da kuma gani da ido, kasancewar akasarin mutane sun fi yarda da abinda suka gani idan aka kwatanta da wadda ji kawai.


Sai dai kasancewar Talabijin na tafiya da zamani ga kuma bukatar wutar lantarki, domin haka ake ganin cewa amfanin da Talabijin ko kuma dogaro dashi ba abu ne da ya zama wajibi ba a kasashe masu tasowa ganin yadda ake fama da karancin wutar lantarki.


Sai dai wannan lamari ya kau domin kuwa yanzu akwai kafofi da dama na kallon Talabijin, domin ci gaban zamani akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajen isar da sako na Talabijin, misali ta wayar hannu ana iya kallon Talabiji

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan