Shekaru 73 Na Atiku Abubakar: Me Ka Sani Game Da Gwagwarmayar Siyasar sa?

192

Manomi, Ɗankasuwa, Kwastam, Ɗansiyasa, Basarake, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007. Alhaji Atiku Abubakar mutum ne jajirtacce, cikakke kuma fitaccen ɗan fafutikar neman ‘yanci. Ya yi fice ƙwarai wajen tallafawa jama’a.

Ya rayu rayuwar aikin kwastam tsawon shekaru ashirin, ya fara aiki a garin Legas, garin da ya samu horonsa na kwastam, ya zauna a Kano , Maiduguri, Kaduna sannan ya sake komawa Legas. Ya yi aiki da shugabannin ƙasar nan har guda shida.

Atiku Abubakar yana daya daga jiga-jigan mutanen da suka kafa jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasar yau ya ke cika shekaru 73 da haihuwa

An haifi Atiku Abubakar GCON ranar 25 ga Nuwambar 1946, ya kasance jigon dan siyasa kuma hamshakin attajiri a fadin Najeriya.

Tun bayan dawowar mulkin dimokuraxiyya cikin shekarar 1999, Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasa na 11, a mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007.

Tun cikin shekarar 1998 aka zabe shi Gwamnan Jihar Adamawa. Daidai lokacin da yake a matsayin zababben Gwamnan, sai zababben shugaban kasa ya zabe shi domin ya mara masa baya a matsayin mataimakin shugaban kasa.

A fannin siyasa, Alhaji Atiku Abubakar gawurtaccen ɗan siyasa ne. Tarihin siyasarsa yana komawa tun daga shekarunsa na karatun difiloma da ya yi a Kano, wato shekarar 1966 zuwa 1967 aka fara zaɓarsa muƙami na farko a matsayin shugaban ɗalibai.

Amma shigarsa siyasar mai ɗungurumgum, ya samo asali ne bayan haɗuwarsa da marigayi Shehu Musa ‘Yar’aduwa wanda shi ya gayyace shi zuwa harkar siyasa daga baya kuma ya zama ubangidansa a harkar siyasa.

Alhaji Atiku Abubakar su suka kafa jama’iyyar ‘People’s Front of Nigeria (PFN)’ tare da su marigayi Shehu Musa ‘Yar’aduwa a watan Mayu na shekarar 1989 bayan cire takunkumin kafa jama’iyyun siyasa da tsohon sugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi.

Jama’iyyar da shi Alhaji Atiku Abubakar ya zamar mata ɗaya daga cikin ‘National Vice Chairmen’. Wannan jama’iyya tasu kamar sauran jama’iyyu, ta ci karo da waigin da shugaba Ibrahimi Badamasi Babaginda ya jefawa ƙungiyoyin siyasa a ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 1989 yana mai cewar gwamnatinsa ba za ta yi wa kowace ƙungiyar siyasa rijis ba, saboda tsofaffin ‘yan siyasa wanɗanda suka dagula lamura su ne suka sake haɗa waɗannan ƙungiyoyi, saboda haka duk ya rushes u ya kafa nasa guda biyu; ‘National Repubican Convention (NRC)’ da kuma ‘Social Democratic Party (SDP)’.

Faruwar wannan al’amari bata karyawa Alhaji Atiku Abubakar da sauran mutane guiwa ba a kan aniyar su ta kawo ƙarshen mulkin soja da kuma ɗora ƙasar Najeriya a kan turbar dimokuraɗiyya.

Alhaji Atiku Abubakar da ubangidansa a siysasa marigayi Alhaji Shehu Musa ‘Yar’aduwa sai suka zaɓi su tsudunma cikin jama’iyyar SPD. To tun daga wannan lokaci har zuwa yau ɗin nan (2019) ake damawa da Alhaji Atiku Abubakar yake kuma bada muhimmiyar gudunmawa wajen ganin dimokuraɗiyya ta zauna da gindinta a Najeriya.

A bangaren harkar iyali kuwa Alhaji Atiku Abubakar, ya auri Titilayo Albert a matsayin matarsa ta farko a shekarar 1971 a garin Legas, sannan kuma ya auri Sa’adatu Ladi Yakubu a matsayin matarsa ta biyu a garin Kano. Sai kuma a cikin shekarar 1983 ya auri Gimbiya Rukaiyat wacce take ‘ya ce ga Lamiɗon Adamawa, Lamiɗo Aliyu Musɗafa, a matsayin matarsa ta uku. Ya yi aurensa na huɗu a ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 1986 inda ya auri Fatima Shettima wanda shi kuma aka ɗaura shi a Maiduguri. Sannan kuma a lokacin da yake gudun hijira a ƙasar Amurka, ya auri Jennifer Iwenjiora bayan ya saki Ladi, wanda hakan ne ya bashi damar yin wannan aure da Jennifer wacce daga baya ta canja sunanta zuwa Jamila Atiku Abubakar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan