Hadakar kungiyar dalibai ta yan arewacin kasar nan (ANNS) ta karrama Farfesa Ladi Sandra Adamu a matsayin Sarauniyar Matan Arewa.



Tun da farko Farfesa Ladi ce ta sanya hotunan yadda aka karramata da wannan matsayi a shafinta na fasebuk.
An karrama Farfesa Ladi Sandra bisa irin gudunmawar da ta ke baiwa ilimi a arewacin kasar nan, sannan kuma ita ce Farfesa ta farko a arewacin kasar nan a bangaren sadarwa.
Tun da farko Farfesa Ladi Sandra Adamu malama a sashen koyar da aikin jarida na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Sannan kuma ita ce mace ta farko a arewacin kasar nan a fannin Sadarwa.
Turawa Abokai