Tunanin ‘Yan Kwankwasiyya Kadan Ne – Janaral Idris Bello Dambazau

1102

Tsohon kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Kano Janar mai ritaya Bello Idris Dambazau ya bayyana magoya bayan injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso wato yan kwankwasiyya a matsayin masu karamin tunani.

Janaral Dambazau ya bayyana hakan ne cikin wani shirin siyasa da ake gabatarwa a gidan radiyon Rahama da ke Kano

“Yan Kwankwasiyya tunaninsu karami ne tuntuni, mu din nan da mu ka baro Kwankwasiyya mu shida. Da Ni (Idris Bello Dambazau) da Aminu Dabo da Farfesa Hafiz da Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya da Isa Zarewa da Babangida Sulen Gar, mun baro domin zalunci da aka yi mana” in ji Idris Dambazau

Haka kuma ya zargi tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da siye dukkanin wani form na yin takara, tare da ajiye shi a gurinsa yana baiwa wanda ya ga dama tare kuma da juya shi yadda ya ke so.

A karshe ya bayyana cewa babban dalilinsu na komawa Gandujiya shi ne su hada kai da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje su kayar da Kwankwasiyya da jam’iyyar su da yan takarkarinsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan