Buhari Ya Buƙaci Majalisa Ta Sahale Masa Ciyo Bashin Dala Biliyan $30

117

Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙara aikawa da wasiƙa zuwa ga Majalisar Dattijai don ta sahale masa ƙudirin ciyo bashi na dala biliyan $30 mai suna 2016-2018 External Borrowing Plan.

Majiyarmu ta ruwaito cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattijai ta 8, Bukola Saraki ya yi watsi da buƙatar ciyo bashin bisa rashin ƙwararan dalilai.

A ranar Alhamis ne Shugaban Ƙasar ya ƙara gabatar da buƙatar ciyo bashin ga Majalisar Dattijan, a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattijan, Ahmad Lawan ya karanta.

A wasiƙar buƙatar ciyo bashin, Shugaba Buhari ya sanar da Majalisar Dattijan cewa za a yi amfani da bashin ne don samar da kuɗaɗe ga ayyuka a ɓangaren wutar lantarki, aikin gona, hanyoyi da ɓangaren ma’adinai.

Shugaban Ƙasar ya tuna cewa Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC, ta amince da ƙudirin ciyo bashin na 2016-2018 tun a shekarar 2016, kuma an aika da shi zuwa ga Majalisar Dattijan a cikin watan Nuwamba, 2016.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan