A ƙalla mazauna gidan yari 30 ne dake zaman waƙafi daban-daban a Gidan Gyaran Hali na Jos ke zana Jarabawar Kammala Babbar Sakandire ta Nuwamba/Disamba, a cewar wata jami’a.
Jami’ar Huɗɗa da Jama’a ta Rundunar Gyaran Hali ta Ƙasa ta Jihar Filato, Martha Banda, ta bayyana haka ga manema labarai ranar Alhamis a Jos.
A cewar Misis Banda, mazauna gidan gyaran halin 30, waɗanda ke zana jarrabawar da Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Ƙasa, NECO ke shiryawa, sun ƙunshi maza 28 da mata biyu.
Ta bayyana cewa hakan yana daga ƙoƙarin Hukumar na mayar da mazauna gidan yarin su zama masu amfanar kansu da kansu, iyalansu da al’umma gaba ɗaya bayan sun kammala zaman waƙafinsu.
“Wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarinmu don bunƙasa tsarin gyaran hali na mazauna garin yarin don su amfani kansu da al’umma gaba ɗaya bayan sun kammala zaman waƙafi.
“Kamar yadda ake cewa ‘Ilimi gishirin zaman duniya’, babban maƙasudin samar da makaranta a gidan yarin shi ne a gyara tarbiyyar mazauna gidan da sana’o’i a kuma ba su ilimin boko”, in ji ta.
Misis Banda ta gode wa ɗai-ɗaikun mutane, Ƙungiyoyin da ba na Gwamnati ba, NGOs, ƙungiyoyin addini da hukumomin gwamnati da suka bayar da tallafin kuɗaɗe da aka yi amfani da su don yi wa mazauna gidan yarin rijistar jarrabawar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa jarrabawar da aka fara ranar 18 ga Nuwamba, za a kammala ta ranar 18 ga Disamba.