Messi Ya Buga Wasanni 700 Daidai

114

Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kuma dan asalin kasar Argentina wato Leonel Messi ya buga wasansa na 700 a jiya wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Brussia Dortmund agasar zakarun nahiyar turai.

Inda awasan Barcelona ta lallasa Dortmund daci 3 da 1 inda Messi ya jefa kwallo awasan.

Daga cikin wasanni 700 da Leonel Messi ya fafata ya jefa kwallaye 613.

Haka dai Messi ya tallafa anjefa kwallaye 237.

Messi bai tsaya nan ba inda ya lashe kofuna har 34 daga cikin wasanni 700 daya buga.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan