Najeriya Ce Ƙasar Da Ta Fi Kowace Ƙasa Noman Doya A Duniya- FAO

462

Hukumar Kula da Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO, ta sa Najeriya a matsayin ƙasar da tafi kowace ƙasa noman doya a duniya, saboda tana samar da kaso 60 cikin ɗari na doyar da ake buƙata a duniya.

Babban Sakataren Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara, Dakta Mohammed Umar Bello, ya bayyana haka a Abuja a Taron Wayar da Kan Kan Noman Doya na Ƙasa da wata ƙungiya mai suna Advocacy and Resource Mobilisation Team, ARMT, na Yam Improvement for Income and Food Security in West Africa, YIIFSWA, wani shiri na International Institute of Tropical Africa, IITA, ta shirya.

Mista Bello, wanda Daraktan Aikin Gona, Injiniya Frank Satumari Kudla ya wakilta, ya lura da cewa koda yake Najeriya tana samar da kimanin kaso 60 cikin ɗari na doya, amma ba ta cikin Ƙasashe Masu Arziƙin Doya saboda rashin ingantaccen iri da kuma samar da irin mai inganci.

Mista Bello ya ce, IITA, ƙarƙashin shirinta na YIIFSWA, ta ga cewa akwai buƙatar ruɓanya fasahar samar da iri wanda za a iya amfani da shi don samar da irin doya mai arha ga manoma don su kuma su samar da doya mai yawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan