Kano Pillars Sun Samo Maki 1 Akan Plateau

256

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tasamo maki 1 awasan mako na 6 ahannun kungiyar kwallon kafa ta Plateau United.

Sun sami maki dayanne bayan sun tashi kunnen doki wato babu ci agarin Jos.

Saidai har yanzu Kano Pillars basu jefa kwallo ba a kakar wasa ta bana ballantana ace su sami maki 3 awasa 1.

Gar yanzu dai Plateau United ne kejan ragamar teburin gasar da naki 14 bayan wasanni 6.

Kano Pillars dai daga jahar ta Jos zasu wuce can jahar Akwa Ibom domin fafata kwantan wasanta da kungiyar kwallon kafa ta Akwa Starlet.

Yanzu dai adadin wasanni 3 da aka baiwa masu horas da Kano Pillars sun kare, inda sukai rashin nasara awasa 1 suka buga kunnen doki awasanni guda biyu.

Shin ko menene makomar masu horas da kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars? biyo bayan ko wasa 1 basuciba awasanni ukun da aka basu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan