Yunwa Ta Yi Ajalin Kananan Yara 29 A Jihar Gombe

516

A kalla kananan yara guda 29 ne su ka rasa rayukansu a jihar Gombe sakamakon rashin cimaka mai kyau.

Jami’in kula da Cimaka na jihar Gombe Sulaiman Mamman ne ya bayyana haka a lokacin gudanar da wani taron magance matsalar yunwa a jihar, ya shaida cewa a watanni 10 na farko shekarar 2019 yara kanana 29 ne yunwa ta kashe a jihar ta Gombe.

Sulaiman Mamman Ya kara da cewar a wannan lokaci a jihar an kai yara kanana sama da dubu 5 zuwa asibitoci sakamakon cutar yunwa in da aka yi wa yara dubu 2,123 magani. Ya kuma ja hankali da cewar sakamakon karancin abinci ya sanya ake fuskantar hatsarin kamuwa da cututtuka da dama.

Ko a shekarar 2017 akwai kimanin yara kanana 150 da su ka mutu a jihar Gombe sakamakon kamuwa da cutar yunwa. Sai dai kuma wasu rahotanni na bayyana cewar sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ta ke kaiwa a yankin arewa maso gabashin kasar nan ya jefa yara kanana kusan miliyan 35 rashin samun wadataccen abinci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan